Aiki Ja: Masu Nadin Sarauta Sun Taka Wa Gwamna Birki Kan Nadin Sabon Sarki
- Wasu daga cikin masu zaben sarki na Oyomesi sun ƙi amincewa da naɗin Abimbola Owoade a matsayin sabon Alaafin na Oyo da Gwamna Seyi Makinde ya amince da shi
- Masu nadin sarautar sun ce sun zaɓi Luqman Gbadegesin ne ba Owoade ba, suna masu cewa tsarin zaben Alaafin ya hana naɗin ta hanyar tuntuba ko son rai
- Gamayyar dattawan sun nemi gwamnan ya janye matakinsa ko kuma su garzaya kotu, suna mai kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Seyi Makinde ya amince da nadin sabon Alaafin na Oyo a yau Juma'a 10 ga watan Janairun 2025
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ibadan, Oyo - Wasu daga cikin masu nadin sarki sun nuna rashin amincewarsu da naɗin Abimbola Owoade a matsayin sabon Alaafin na Oyo.
Dattawan sun kalubalanci Gwamna Seyi Makinde bayan ya amince da nadin a ranar Juma’a 10 ga watan Janairun 2025.
An kalubalanci nadin sabon sarki a Oyo
TheCable ta ruwaito cewa masu nadin sarautar sun sanar a cikin wata wasiƙa da suka aika wa gwamnan a yau Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mambobin kwamitin mai mutum biyar daga cikin bakwai sun bayyana naɗin Owoade a matsayin wanda bai dace ba kuma babu inganci.
Wasu daga cikin waɗanda suka goyi bayan ƙin amincewar sun haɗa da Yusuf Akinade (Basorun), Wakeel Akindele (Lagunna), da Hamzat Yusuf (Akinniku).
Sun ce sun zaɓi Luqman Gbadegesin, ba Owoade ba, kamar yadda tsarin Alaafin na 1967 ya tanada.
“Zaɓen Alaafin ba ta hanyar son rai ko tuntuba ake yi ba, amma bisa ka’idojin da aka tsara a cikin tsarin na 1967.”
- Cewar sanarwar
Masu nadin sarauta sun ba gwamna shawara
Masu nadin sarautar suka ce bashorun na Oyo, shugaban Oyomesi, ne kaɗai ke da haƙƙin kiran taro don zaɓen Alaafin, cewar Punch.
Sun ƙara bayyana cewa babu wani taro da aka gudanar a fadar Alaafin kamar yadda al’ada ta tanada don zaɓar Prince Abimbola Akeem Owoade.
Sun kuma zargi gwamna Makinde da yin watsi da al’adu da tsare-tsaren masarautar Oyo, suna mai cewa duk wani taro da aka gudanar ba bisa ka’ida ba, a ofishin gwamna ko a wani wurin daban, bai da wata madafa ta doka.
Sun nemi gwamnan ya janye matakin nasa ko kuma su garzaya kotu don ƙalubalantar matakin.
A ƙarshe, sun yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu tare da tabbatar da doka da oda a yayin da suke jiran hukuncin kotu.
Kotu ta yi hukunci kan rigimar Kano
Kun ji cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun jihar Kano na ranar 15 ga Yuli, 2024 a kan rikicin masarauta.
Wancan hukuncin ya hana wasu sarakunan gargajiya na Kano amfani da mukamansu bayan gwamnati ta shigar da kara.
Hukuncin babbar kotun ya kuma ce ba shi da hurumin sauraren duk wata Shari'a da ta shafi batun masarautu a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng