Bafade Mafi Tsufa a Masarautar Alaafin Na Oyo, Baba Keji Ya Kwanta Dama

Bafade Mafi Tsufa a Masarautar Alaafin Na Oyo, Baba Keji Ya Kwanta Dama

  • Rahoton da muka samo daga majiya ya bayyana cewa, Allah ya yiwa wani fitaccen Bafade a masarautar Alaafin na Oyo rasuwa
  • Allah ya dauke Morenikeji Lasisi bayan shafe shekaru 120 a duniya, ya shafe shekaru 77 yana bauta a fadar Alaafin
  • Rahoto ya bayyana kadan daga tarihinsa da kuma tasirinsa a masarautar ta Alaafin da ke Oyo a Kudu maso Yammacin Najeriya

Jihar Oyo - Morenikeji Lasisi, Bafade mafi tsufa a cikin fadawan Alaafin na Oyo wanda aka fi sani da ‘Baba Keji’ ya kwanta dama.

Rahoton Vanguard ya bayyana cewa, Lasisi ya rasu yana da shekaru 120 a duniya, kuma ya yi bauta a fadar Alaafin na tsawon shekaru 77, inda ya kwanta dama ranar Litinin 13 Faburairu, 2023 a fadar ta Oyo.

Sai dai, wata tattaunawa da jaridar The Guardian ta yi da Baba Keji ta nuna cewa, shi kansa bai san adadin shekarunsa, kawai dai ya yi kirdadon lokacin da yake da wayau ne.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Shugaba Buhari ya Dira Hedkwatar Tsaro don Aiwatar da Muhimmin Aiki

Allah ya yiwa Bafade mafi jimawa a fadar Alaafin rasuwa
Bafade Mafi Tsufa a Masarautar Alaafin Na Oyo, Baba Keji Ya Kwanta Dama | Hoto: Arewa Omo'ba, Oba Lamidi Adeyemi III
Asali: Facebook

Rasuwarsa na zuwa ne watanni 10 kacal bayan rasuwar Oba Lamidi Adeyemi III, wanda ya yi mulki a fadar na tsawon shekaru 51.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanene Baba Keji da kuma tasirinsa a masarautar Alaafin na Oyo

Ana yiwa Baba Keji kallon Bafade dan amana kuma mai juriya da aiki tukuru ga masarautar Alaafin na Oyo.

A cewar wasu daga cikin fadawan:

“Yana yin aikin da aka saka shi, ba gajiyawa, kamar yadda Alaafin ya umarta.”

Ya kuma yi shuhura a matsayin abokin tafiyar Alaafin a cikin fadar, wanda kuma aka ce ya tattara tarin sani game da tarihin baya na masarautar da tsatsonta.

Hakazalika, ana yiwa Baba Keji kallon wata taska ta ilimin masarautar Oyo mai dimbin tarihi.

Allah ya yiwa Alaafin na Oyo rasuwa

A wani labarin na baya, kunji yadda duniya ta kadu da samun labarin rasuwar Alaafin na jihar Oyo bayan shafe shekaru yana mulki.

Kara karanta wannan

Karya Ne, Babu Wanda Ya Yiwa Mai Mala Buni Rajamu: Ahmad Lawan

An ruwaito cewa, fitaccen basaraken ya rasu ne a ranar 23 ga watan Afrilu, kuma nan take aka fara shirin jana'izarsa.

Oba Lamidi Adeyemi III, ya rayu shekaru 81 a duniya, ya shafe shekaru sama da 51 yana mulki a masarautar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.