Yan Bindiga Sun Far Wa Jami'an Tsaro, Sun Hallaka Sama da 20 a Jihar Katsina
- Dakarun rundunar askarawan Katsina da ƴan banga sun faɗa tarkon ƴan bindiga a kauyen Baure da ke ƙaramar hukumar Safana a Katsina
- An ruwaito cewa ƴan ta'addan sun hallaka dakarun rundunar haɗin guiwa akalla 21 tare da wasu fararen hula da harin kwantan ɓauna
- Rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce waɗanda aka kashe sun dawo ne daga ta'aziyya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 21 a wani mummunan harin kwantan ɓauna da suka kai a jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma.
Ƴan ta'addan sun hallaka dakaru 21 na rundunar haɗin guiwa da ta kunshi askarawan Katsina da ƴan banga a kauyen Baure da ke ƙaramar hukumar Safana.
Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Katsina, Sadiq Abubakar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce harin ya faru ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a kauyen Baure, yankin ƙaramar hukumar Safana ta Jihar Katsina.
Ƴan bindiga sun kashe masu ta'aziyya
Sadiq ya ce waɗanda aka kashe sun dawo ne daga ta'aziyya lokacin da ake zargin 'yan bindigar suka yi musu kwanton bauna.
Ya ƙara da cewa an tura jami'an tsaro yankin domin dawo da zaman lafiya, kuma ana ci gaba da bincike don kama waɗanda suka aikata wannan ta'addanci.
Shaidu sun nuna cewa kimanin mutane 25 ne suka rasa rayukansu a harin, yayin da har yanzu wasu mazauna kauyen ba a gansu ba.
Mutanen da aka kashe sun wuce 20
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa yankin da abin ya faru ya yi ƙaurin suna a matsayin mafakar 'yan bindiga.
"Jiya sun kai harin kwanton bauna a titin, suka budewa motar da ke ɗauke da 'yan banga wuta, suka kashe wasu daga cikinsu.
"Bayan kwanton baunar, 'yan bindigar sun yi amfani da ranar kasuwa, suka bi mutane har gidajensu, suka kashe da dama.
"Daga ƙididdigar da aka yi zuwa yanzu, an tabbatar da mutuwar mutane sama da 15, kuma har yanzu wasu da dama ba a gansu ba."
Harin ya shafi garuruwa da dama a Katsina
Wani mazaunin yankin ya ce galibin waɗanda aka kashe sun fito ne daga garuruwan Charanci, Burji, Jibiya da ƙaramar hukumar Kaita.
"Mun ceto fiye da mutane 20 a harin. Wasu daga cikin waɗanda aka kashe sun fito ne daga Charanci, Burji, Jibiya, da ƙaramar hukumar Kaita.
"A yanzu, an tabbatar da mutuwar mutane 25, yayin da har yanzu wasu ba a san inda suke ba," in ji shi.
An kashe hatsabibin ɗan bindiga
A wani labarin, kun ji cewa dakarun tsaro sun yi nasarar murƙushe ƙasurgumin ɗan bindiga da ya danu al'umma a Katsina.
Bako Baƙo ya mutu ne a lokacin da dakarun rundunar tsaro ta Najeriya ta kai samame maɓoyarsa.
Asali: Legit.ng