An Shiga Jimami da Tsohon Shugaban Majalisar Dokoki Ya Yi Babban Rashi
- Mahaifiyar tsohon shugaban majalisar wakilai, Dimeji Bankole, ta yi bankwana da duniya bayan fama da rashin lafiya
- Dattijuwar mai suna Monsurat Bankole, ta rasu ne a ranar Juma’a 10 ga watan Janairun 2025 bayan shafe rayuwarta kan tafarkin addini
- Monsurat Bankole ita ce Iya Adinni a yankin Egba, kuma ta kafa kungiyar Al Mönsur Islamic Society
- Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya yi alhinin rasuwar marigayiyar inda ya bayyana irin gudunmawar da ta bayar a bangaren addini
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Abeokuta, Ogun - Mahaifiyar tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Dimeji Bankole ta riga mu gidan gaskiya.
Marigayiyar Monsurat Bankole ta rasu ne a yau Juma'a 10 ga watan Janairun 2025 bayan fama da jinya mai tsawo.
Tsohon kakakin Majalisa ta rasa mahaifiyarsa
Vanguard ta ruwaito cewa marigayiyar da ta rasu a yau Juma'a ta rasa ranta ne tana tsaka da ba da gudunmawa ga addinin Musulunci da al’umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Monsurat Bankole ita ce Iya Adinni ta garin Egba kafin rasuwarta, kuma ta yi fice wajen sadaukar da rayuwarta don ci gaban addini da al'umma.
Wani malamin addini da ke matsayin mai ba wa Gwamnan Ogun shawara, Sheik Iskeel Lawal, ya sanar da rasuwar ta a cikin wata sanarwa.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa marigayiyar ta kafa kungiyar Al Mönsur Islamic Society kuma tana da mukamin Iya Sunnah na Alasalatu Society of Nigeria.
Sheik Iskeel ya ce za a yi jana’izarta daidai da koyarwar Musulunci bayan sallar la’asar ranar Juma’a a gidan mijinta marigayi da ke Onikoko a Abeokuta.
Gwamnan Ogun ya yi alhini
Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya yi ta’aziyya ga Dimeji Bankole bisa wannan babban rashi, yana bayyana mahaifiyarsa a matsayin shugabar al’umma mai nagarta.
A cikin sakon ta’aziyyarsa, Gwamnan ya ce Monsurat Bankole ta zama ginshiki mai karfi ga iyalanta, kuma ta yi fice wajen hidimar al’umma da kuma addini.
Haka zalika, ya yaba da rawar da ta taka wajen ciyar da al’umma gaba, yana addu’ar Allah ya ba ta Aljanna Firdausi, cewar The Nation.
Yayin da yake nuna alhini, ya ce jihar Ogun ta rasa wata jaruma mai karfin zuciya, musamman bayan rasuwar Madam Adebisi Edionseri da ake kira 'Cash Madam.'
Ya bayyana cewa kowa na jin saukin rashi ne ta hanyar kyawawan ayyukanta na addini da taimakon jama’a, kuma Allah ya saka mata da Aljanna Firdausi.
Kwamishina a Cross River ya rasu
A baya, kun ji cewa kwamishinan harkokin yawon buɗe idanu, al'adu da fasaha na jihar Cross River, Abubakar Ewa ya rasu ranar Laraba, 8 ga watan Janairu, 2025.
Rasuwar tsohon kwamishinan ta girgiza al'ummar jihar Cross River kasancewar marigayin ya halarci taron majalisar zartarwa wanda Gwamna Bassey Otu ya jagoranta a ranar.
An ruwaito cewa galibin abokan aikinsa a gwamnatin CrossRiver sun je asibitin da ya rasu domin yi wa ƴan uwa da abokan arziki ta'aziyya.
Asali: Legit.ng