Bayan Barazanar Kwamushe Shi da Sojoji Suka Yi, an Gano Bello Turji Yana Neman Tsira

Bayan Barazanar Kwamushe Shi da Sojoji Suka Yi, an Gano Bello Turji Yana Neman Tsira

  • An gano rikakken dan ta'adda Bello Turji da yaransa sun kwana suna dasa wasu abubuwa a kusa da duwatsun Fakai da Manawa don kare kansu daga hare-hare
  • Duwatsun Fakai da Manawa sun zama mafaka ga Turji da tawagarsa duk lokacin da suka ji barazanar farmaki daga jiragen soja ko idan suna shawagi
  • Yan tawagar sun tsara wannan aikin ne don kare kansu yayin da suke tsoron hare-haren sojoji musamman a yanzu da ake musu barazana
  • Yan tawagar sun tsara wannan aikin ne don kare kansu yayin da suke tsoron hare-haren sojoji ko jiragen

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gusau, Zamfara - Rahotanni sun tabbatar da cewa an gano Bello Turji da mayakansa sun kwana suna dasa wasu abubuwa a kusa da duwatsun duwatsun Fakai da Manawa domin tsare kansu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bi kauyuka suna yanka mutane da wuka, sun kashe rayuka

Wadannan duwatsu sun kasance wurin da suke boyewa duk lokacin da suka lura akwai barazanar hare-hare ko suka hango jiragen saman yaki na sojoji.

Bello Turji ya nemo hanyar tsira daga hare-haren sojoji
Dan ta'adda, Bello Turji ya rikice bayan barazanar sojoji. Hoto: Legit.
Asali: Original

Sojoji sun yi wa Bello Turji barazana

Shafin Zagazola Makama shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 10 ga watan Janairun 2025 a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan rundunar sojoji ta yi barazanar Kawo karshen Bello Turji nan ba da jimawa ba domin dakile ayyukan ta'addanci.

Sojojin rundunar Operation Fansar Yamma sun tabbatar da cewa Bello Turji yanzu yana rayuwa kamar beran daji yana buya a rami.

Sojoji sun farmaki sansanin Bello Turji

Rundunar ta kai farmaki kan sansaninsa da ke Karamar Hukumar Shinkafi, inda jiragen yakin sojoji suka lalata sansaninsa.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda ciki har da kashe wani shahararren dan ta’adda, Sani Rusu.

Kara karanta wannan

Masu ritaya: An gano miliyoyin Naira da gwamnati za ta kashewa manyan jami'an soji

Sanarwar ta tabbatar da cewa Bello Turji da mayakansa suna yawan amfani da duwatsun domin kare kansu, cewar Daily Post.

Bello Turji ya fara neman hanyar tsira

Aikin dasa abubuwan ya kasance wata dabara da suka bullo da ita don samun kariya yayin da suke tsoron fuskantar farmakin soja daga sama ko kasa.

Wasu majiyoyi suka ce Bello Turji ya shiga mawuyacin hali tun bayan kama wasu daga cikin mataimakansa.

Hakan ne ya tilasta dan ta'addan fara neman yadda zai kare kansa duba da barazanar da sojoji ke yi da kuma rage masa karfi da kullum ake yi saboda samun nasara yaki da ta'addanci.

Bello Turji ya caccaki Dauda Lawal

Kun ji cewa kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya soki hukumomin Najeriya kan yada karya da cewa sun kama yan uwansa a wani harin da suka ce sun kai.

Turji ya ce sojoji suna ba yan Najeriya kunya saboda sun je sun kama dattawa a asibitoci amma suna cewa sun kama yan bindiga wanda ba gaskiya a cikin labarin.

Dan ta'addan ya caccaki Gwamna Dauda Lawal Dare inda ya ce yana daga cikin wadanda suka hana jihar Zamfara zaman lafiya da kawo matsalolin na ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.