Sarauta: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yi Hukunci a Rikicin Aminu da Sanusi II
- Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin Kotun Babbar Jihar Kano na ranar 15 ga Yuli, 2024 a kan rikicin masarauta
- Wancan hukuncin ya hana wasu sarakunan gargajiya na Kano amfani da mukamansu bayan gwamnati ta shigar da kara
- Hukuncin babbar kotun ya kuma ce ba shi da hurumin sauraren duk wata Shari'a da ta shafi batun masarautu a fadin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke umarnin da Kotun Babbar Jihar Kano ta bayar, wanda ya hana wasu sarakunan gargajiya na Kano kiran kansu a matsayin sarakuna.
Wani kwamitin alkalai uku, karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Mustapha, ya bayyana cewa hukuncin Kotun Kano na ranar 15 ga Yuli, 2024 ya ci karo da ka’idojin adalci ga kowane bangare.
Premium Times ta wallafa cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa akwai tangarda a cikin umarnin da Kotun Kano ta bayar ta fuskar cika ka’idojin shari’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta kara da janye hukuncin da ya hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da sauran sarakunan Bichi, Rano, Gaya, da Karaye, amfani da mukamansu na gargajiya.
Kotu ta yi umarni a kan dambarwar sarautar Kano
Justice Watch News ta wallafa cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta umarci babbar alkaliyar Jihar Kano ta sake bai wa wani alƙali daban shari’ar rikicin masarautar Kano domin ci gaba da sauraro daga farko.
Wannan hukunci dai bai kawo karshen dambarwar masarautar da ta-ki-ci, ta-ki-cinyewa ba tun bayan da gwamnatin Kano ta tube rawanin Sarakunan jihar guda biyar.
Rikicin sarauta: Martanin lauyan gwamnatin Kano
Da yake magana da majiyar Legit , lauya mai kare gwamnati, Barista Bashir Tudun Wuzirce, ya ce kotun ta tabbatar da cewa ba ta da hurumin yin hukunci kan lamarin.
Ya kara da cewa:
“Alhamdulillah, wannan ba karamar nasara ba ce kamar yadda kullum muke ta fada, dama ita babbar kotun tarayya ba ta da hurumi a kan abin da ya shafi harkar masarauta. Harka ce wadda sai dai kotun jiha.”
“Kuma duk abin da ya shafi abin da majalisar jiha za ta yi doka a kai, babbar kotun jiha ta Kano ce kawai za ta yi wannan hukunci, kuma shi ne abin da kotun Abuja ta tabbatar.”
Ya ce wannan ta tabbatar da cewa dokar majalisar dokokin jiha ta na nan, kuma Sarki na 1, Muhammadu Sanusi II ne halastaccen Sarkin Kano.
Kotu ta yi hukunci a rikicin masarautar Kano
A baya, kun ji cewa babbar kotun ta haramta wa Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan masarautun Bichi, Rano, Gaya, da Karaye kiran kansu sarakuna.
An yi zaton wannan hukunci na iya kawo ƙarshen rikicin masarautar Kano, sai dai ɓangarorin da abin ya shafa su dauki matakin ɗaukaka ƙara domin a neman wani hukunci.
Asali: Legit.ng