Rundunar 'Yan Sanda Ta Yi Bayani a kan Sace Sama da N1bn daga Asusun Gwamnati
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa babu wani kutse da aka yi cikin asusun Gwamnatin Jihar Enugu
- Mai magana da yawun 'yan sandan, Muyiwa Adejobi, ya bayyana cewa an gudanar da binciken a kan zargin kutsen
- Rundunar 'yan sandan ta yi kira ga 'yan Najeriya da su daina yada labaran karya kuma su tabbatar da sahihancinsa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Enugu - 'Yan sandan kasar nan sun musanta rahotannin da ke cewa wani dan fashin intanet ya shiga asusun Gwamnatin Jihar Enugu tare da satar N1.09 biliyan.
An samu labarin cewa wani shahararren dan fashin intanet da ake zargin sunansa Osita Onuma, ya kutsa asusun gwamnatin jihar Enugu, har ya kwashe makudan kudin.
Premium Times ta ruwaito cewa ana zargin ‘yan fashin intanet din sun sace akalla N1,097,700,300 daga asusun gwamnatin jihar, lamarin da ya jefa jama'a a cikin rudani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan sanda sun gudanar da bincike
Jaridar Punch ta wallafa cewa Adejobi ya ce Cibiyar Yaki da Laifukan Intanet ta Ƙasa (NCCC) ta gudanar da bincike ka zargin kutse ta intanet a asusun gwamnati.
Ya ce:
“An kama wanda ake zargi a dangane da wannan zamba, kuma an dawo da kudaden."
“Gwamnatin Jihar Enugu da sauran ma’aikatu, sassa, da hukumomin gwamnati da kamfanoni suna aiki tare da NCCC kuma sun kafa tsare-tsaren tsaro masu karfi don kare tsarin kudinsu.”
‘Yan sanda sun karyata kutse a asusun gwamnati
A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Alhamis, mai magana da yawun ‘yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya bayyana rahoton a matsayin karya da ya dade ya na yawo, kuma babu hujja a ciki.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ta ce;
“Babu wani kutse da aka yi cikin asusun Gwamnatin Jihar Enugu, kuma zargin satar kudi har N1.09 biliyan ba shi da tushe.”
‘Yan sanda sun yi gargadi game da labaran karya
Rundunar ‘yan sandan ta gargadi al’umma da su daina yada labaran da ba su tabbatar da ingancinsu ba.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina yada bayanan karya da su tabbatar da sahihancin tushe kafin su yada su.
'Yan sanda sun sheke dan ta'adda
A wani labarin, kun ji cewa jami'an tsaro a jihar Katsina sun samu nasarar hallaka wani gawurtaccen shugaban ƴan bindiga, Baƙo Baƙo, a cikin wani farmaki da suka kai a ƙaramar hukumar Batsari.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaron sun gudanar da farmakin a kan Bako Bako da tawagar mayaƙansa a maɓoyarsa bayan dogon lokaci na farautar fitinannen dan ta'addan da ya addabi jama'a.
Mutanen yankin Batsari sun nuna matuƙar farin ciki kan wannan nasarar da jami'an tsaron suka tabbatar da tsaro a yankin bayan suna fama da hare-haren wannan shugaban ƴan bindiga na tsawon lokaci.
Asali: Legit.ng