Kotu Ta Hana Belin Tsohon Jami'in Gwamnatin El Rufa'i da Aka Garkame

Kotu Ta Hana Belin Tsohon Jami'in Gwamnatin El Rufa'i da Aka Garkame

  • Kotu ta hana belin tsohon shugaban ma’aikata na tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, Muhammad Bashir Sa’idu,
  • An kama Sa’idu ne a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, sannan aka gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Majistare da ke Rigasa
  • Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta zargi Sa’idu karkatar da wasu kudade da aka samu a wajen cefanar da kadarar gwamnati

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Kotu ta hana belin tsohon shugaban ma’aikatan fadar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, Muhammad Bashir Sa’idu a yayin da ake ci gaba da shari’a.

An gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin almundahana, inda babbar Kotun Jihar Kaduna ta dage yanke hukuncin kan neman belin Sa’idu zuwa ranar 16 ga Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Lambar El Rufai ta fito a tuhumar da ake yi wa tsohon jami'in gwamnatin Kaduna

Kaduna
An ci gaba da tsare tsohon jami'in gwamnatin Kaduna Hoto: Nasir El Rufa'i/Bashir Sa'idu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an kama Sa’idu ne a ranar 30 ga Disamba, 2024, a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, sannan aka gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Majistare da ke Rigasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin almundahana a gwamnatin El-Rufa’i

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Sa’idu ya amince da sayar da kadarar gwamnati a kan dala miliyan 45 kimanin Naira biliyan 18.4.

Ana ganin wannan ya yi kasa da farashin da ya dace na Naira biliyan 498, wanda hakan ya janyo wa gwamnatin jihar asarar Naira biliyan 3.9 a shekarar 2022.

An jami’in gwamnatin El Rufa’i da almundahana

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta zargi Sa’idu da karkatar da Naira biliyan 3.9, wanda ya saba wa Sashe na 18 na Dokar Hana Almundahana ta Shekarar 2022.

Sai dai lauya mai kare Sa’idu, Oladipo Tolani (SAN), ya musanta wadannan zarge-zarge, yana mai cewa basu da tushe ballantana makama.

Kara karanta wannan

Tsohon jami'in gwamnatin El Rufai ya shiga matsala, bayan ICPC ta maka shi kotu

Martanin jami’in gwamnatin Kaduna

Lauyan Sa’idu, Oladipo Tolani ya bayyana cewa wanda ya ke wakilta bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba, sannan bai kira sunan Nasir El Rufa'i a shari’ar da ake yi ba.

Kan ikirarin da ke cewa Sa’idu ya ambaci tsohon shugaban sa a gaban kotu, Tolani ya ce: ‘Duk wanda ya fadi hakan ya yi karya ne kawai.

“Mun gabatar da bukatar neman beli wadda aka tattauna a yau (jiya). A halin yanzu, gwamnatin jihar ta shigar a kara a kan Sa’idu. An dage shari’ar zuwa 16 ga Janairu, 2025, don yanke hukunci.”

Tsohon jami'in gwamnatin Kaduna ya ba da bayanai

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Jihar Kaduna a lokacin mulkin Nasir El-Rufa’i, Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu, ya bayar da bayanai

Ana zargin daga cikin muhimman bayanai a kan tuhumar almundahana da ake yi masa, Sa'idu ya ambaci sunan tsohon gwamnan, Malam Nasir El-Rufa’i, a jawabin sa ga jami’an tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.