Majalisa Ta Kalubalanci Gwamnatin Tinubu Ta Nuna Aikin da Ta Yi da Kudin Tallafin Mai
- Rahotanni sun nuna cewa Sanatoci sun nuna damuwa kan aiwatar da kasafin kuɗin 2024, musamman batutuwan kashe kuɗin tallafin man fetur
- Sanata Abdul Ningi ya buƙaci Ministocin Kuɗi da Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi su bayyana adadin kudin da aka tara daga ribar cire tallafin mai
- Sanata Tahir Monguno ya yi kira da a sake duba tsarin da ake bi wajen aiwatar da kasafin kuɗi domin samun damar yin ayyuka a kan lokaci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sanatoci sun nuna damuwa kan aiwatar da kasafin kuɗin 2024, yayin wata tattaunawa da Ministocin Kuɗi da Kasafin Kuɗi, Wale Edun da Atiku Abubakar Bagudu.
Kwamitin Kasafin Kuɗin Majalisar Dattawa ya yi kira da a yi cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da kudin da aka samu daga cire tallafin mai a 2024.
Tribune ta wallafa cewa Sanatocin sun bayyana rashin gamsuwarsu da yadda aka sarrafa kudin manyan ayyuka da aka ware a 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kalubalanci minista kan tallafin mai
Shugaban kwamitin kasafi, Sanata Solomon Olamilekan Adeola, ya yi tambayoyi kan yadda ake kashe kuɗin da aka ware domin ayyukan raya ƙasa da kuɗin da aka samu daga cire tallafin mai.
Sanata Abdul Ningi ya buƙaci Ministocin da su bayar da cikakken rahoto kan adadin kuɗin da aka samu daga cire tallafin mai da kuma yadda aka kashe su.
“Muna buƙatar a bayyana mana yawan adadin kuɗin da aka kashe wajen biyan basussuka a kasafin kuɗin 2024,"
- Sanata Abdul Ningi
Sanatan ya kuma tambayi ministocin kan tasirin tsawaita aiwatar da kasafin kuɗin 2024 zuwa watan Yunin 2025 kan tattalin arzikin ƙasa.
Premium Times ta wallafa cewa bayan tambayoyin, Ministan kudi, Wale Edun ya bukaci tattaunawa da 'yan majalisar ta bayan fage.
Wale Edun ya bukaci a sallami 'yan jarida daga wajen tattaunawar wanda hakan ya sansa gaza gano amsar da ya bayar a bayan fage.
Bukatar sauya tsarin aiwatar da kasafin kudi
Sanata Tahir Monguno, ya bayyana cewa tsarin da gwamnatin Tinubu ta kirkiro na aiwatar da kasafin kudi yana kawo tsaiko ga aiwatar da kasafin kuɗi.
Tahir Munguno ya ce tsarin ya maida hankali kan Ofishin Akanta Janar na Ƙasa, wanda ya sauya tsarin da a baya ake amfani da shi inda ma’aikatu daban-daban ke kula da ayyukansu da kansu.
A cewar Sanatan, sauya tsarin ya janyo tsaiko da kuma yiwuwar samuwar cin hanci saboda mika iko kan kasafi ga ofishin Akanta Janar.
A karkashin haka, Sanatan ya yi kira ga gwamnati da ta sake duba wannan tsari domin tabbatar da aiwatar da ayyukan raya ƙasa cikin sauƙi da nagarta.
Damuwa kan Jinkirin gabatar da kasafi
Sanata me wakiltar Benue ta Tsakiya, Abba Moro ya nuna damuwa kan jinkirin gabatar da kasafin kuɗi daga bangaren zartarwa.
Abba Moro ya ce jinkirin gabatar da kasafin kuɗi na iya kawo cikas ga tsarin gudanar da kasafin kuɗi daga watan Janairu zuwa Disamba.
APC za ta cigaba da kare Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yi gargadi kan masu yada karya ga gwamnatin Bola Tinubu.
Abdullahi Ganduje ya tabbatar da cewa za su cigaba da kalubalantar duk masu yada karya ga gwamnati tare da fito da gaskiyar abin da ke faruwa.
Asali: Legit.ng