An Shiga Tashin Hankali a Abuja, Wata Mata da Yaronta Sun Ƙone Ƙurmus a cikin Gida

An Shiga Tashin Hankali a Abuja, Wata Mata da Yaronta Sun Ƙone Ƙurmus a cikin Gida

  • Gobara da ta tashi da tsakiyar dare ta kashe wata mata mai shekara 24 da ɗanta mai shekara ɗaya da watanni shida a Abuja
  • Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa wutar ta tashi lokacin da mutanen ke barci, kuma ba a gano abin da ya haddasa gobarar ba
  • 'Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, kuma tuni aka birne mamatan a wata makabarta da ke hanyar Abuja-Nyanya-Keffi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gobara ta kashe wata mata mai shekara 24, Jumai Sunday da ɗanta dan shekara ɗaya da watanni shida, Nasir Rabiu, a Abuja.

Lamarin ya faru ne a wani gida da ke kasuwar kayan ɗaki ta Kugbo, ƙaramar hukumar birni (AMAC) a babban birnin tarayya.

'Yan sanda sun yi magana yayin da gobara ta kashe wata mata da yaronta a Abuja
Gobarar dare ta halaka wata mata da yaronta a birnin tarayya Abuja. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Abuja: Gobara ta kashe mahaifiya da danta

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa matar da yaron nata sun fito ne daga ƙaramar hukumar Eggon ta jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Abuja: Bincike ya yi nisa, an gano wanda ya tashi bom a makarantar Islamiyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu da suka shaida faruwar lamarin sun ce wutar ta tashi yayin da Jumai da ɗanta ke cikin nauyin barci a ranar Laraba, 8 ga Janairun 2025.

Majiyoyin sun ce bayan kashe wutar, maƙwabta da masu taimako sun gano gawarwakin mutanen biyu da suka ƙone kurmus.

'Yan sandan sun tabbatar da tashin gobarar

Ɗan sanda mai kula da sashen Karu, Lakur Langyi, ya tabbatar wa 'yan jarida da faruwar lamarin, inda ya ce sun samu kiran gaggawa a tsakiyar dare.

Lakur Langyi ya ce:

“Eh, tabbas wuta ta tashi a Kugbo a wani wurin da ake kira Bakasi. Mutanena sun gano cewa wata mata da ɗanta sun ƙone.”

Ɗan sandan ya bayyana cewa har yanzu ba a gano abin da ya haddasa gobarar ba, amma sun fara bincike kan lamarin.

Mazauna Abuja sun girgiza da lamarin

Jagoran 'yan sandan na sashen Karu, ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Abin fashewa da ake zaton 'bom' ne ya tarwatse a makarantar islamiyya, ɗalibai sun mutu

“Mutanena sun fara gudanar da bincike kan lamarin, kuma suna nan a yankin don karin bincike.”

Maƙwabta da 'yan uwa sun birne mamatan a makabartar Kugbo da ke kusa da hanyar Abuja-Nyanya-Keffi.

Wannan lamarin ya girgiza mazauna yankin, inda suka bayyana damuwa kan yadda gobarar ta ƙone matar da danta, kuma suka mutu a dare daya.

Gobara ta tashi a kasuwar birnin Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar da ke rukunin gidajen Trademore, Lugbe, Abuja, a daren Lahadi, 1 ga Disamba, 2025.

Gobarar ta tashi ne a kasuwar guda ɗaya tilo da ke rukunin gidajen, da misalin ƙarfe 3:30 na dare bayan dawo da wutar lantarki.

Gobarar ta mamaye kasuwar kafin jami’an agaji su isa wurin, sai dai har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

Shaidu sun zargi matsalar wutar lantarki da haddasa lamarin, inda Vanguard Joe, wacce ta fara gani, ta bayyana shi a matsayin tashin hankali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.