Yarjejeniyar $2bn: Shugaba Tinubu Ya Roki Arziki da Ya Hadu da Ministan China

Yarjejeniyar $2bn: Shugaba Tinubu Ya Roki Arziki da Ya Hadu da Ministan China

  • Shugaba Bola Tinubu ya nemi ƙara adadin $2bn da aka kulla a yarjejeniyar musayar kudade tsakanin ƙasar nan da China
  • Shugaban ya nemi a sake duba tallafin dala biliyan 50 da China ta ware don Afirka, yana mai cewa akwai bukatu a nahiyar
  • Tinubu ya roki China da ta mara wa Najeriya baya wajen samun kujera ta dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, ya bukaci gwamnatin China da ta kara adadin yarjejeniyar musayar kudade da ke tsakaninsu.

Kasashen biyu sun ƙulla yarjejeniyar Dala biliyan biyu, lamarin da Bola Tinubu ya ke ganin akwai bukatar a ƙara yawan kuɗin zuwa wani mataki na gaba

Kara karanta wannan

Shugaban Ghana ya jefa mutanen duniya a mamaki wajen kiran Tinubu a taro

Tinubu
Tinubu ya karbi bakuncin jakadan China Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

A saƙon da hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun, ya wallafa a shafin X, Tinubu ya bayyana gamsuwarsa kan ziyarar Ministan Harkokin Wajen China, Wáng Yì.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasar ya ƙara nanata muhimmancin dangantakar da ke tsakanin Najeriya da China, musamman ta fuskar samar da ciga da raya ƙasa.

Tinubu na son karin adadin musayar kudade

A yayin ganawar da Wáng Yì, Shugaba Tinubu ya jaddada cewa karuwar adadin musayar kudin za ta taimaka wajen hanzarta ci gaban ayyukan raya kasa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara da cewa;

"Mun bukaci karin hadin kai a fannin musayar kudade. Adadin da aka amince da shi na dala biliyan biyu bai isa ba idan aka duba shirye-shiryenmu.
Idan za ku iya kara wannan adadin, za mu yaba sosai. Ya kamata dangantakarmu ta yi karfi fiye da yadda take yanzu har ta zama mai dorewa."

Kujerar MDD: Tinubu ya nemi taimakon China

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi abin da za ta yi wa wadanda gobarar kasuwar Kara ta shafa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi goyon bayan China wajen tabbatar da samun Najeriya kujera ta dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. Ya kara da cewa:

"China tana daga cikin kasashe masu kujerar dindindin a Majalisar Dinkin Duniya. Muna son ku yi amfani da wannan dama wajen tabbatar da cewa Najeriya ta samu wannan kujera ta dindindin."

Najeriya ta dade ta na fafutukar ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da ke da kujerar ta dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaba Tinubu ya bayyana karfin dangantaka tsakanin Najeriya da China a matsayin mai matukar muhimmanci wajen tabbatar da ci gaba da raya kasa.

Ana Allah-wadai da kuɗin tafiye-tafiyen Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta fuskanci suka daga jam’iyyun adawa, kungiyoyin fararen hula, da wasu masu sharhi kan shirin tafiye-tafiyen Bola Tinubu.

Gwamnatin tarayya za ta kashe Naira biliyan 55 da aka ware domin jiragen shugaban kasa a kasafin kudin shekarar 2025 da Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dokoki ta Kasa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

Jam’iyyar LP, ta bakin mai magana da yawunta, Abayomi Arabambi, ta bayyana matakin a matsayin rashin tausayi da nuna halin ko-in-kula ga matsalolin jama’a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.