Magana Ta Dawo Sabuwa, Kotu Ta ba Ministocin Tinubu 2 Umarni kan Kudirin Haraji
- Babbar Kotun Tarayya ta umarci Ministan Gida da na shari'a su bayyana gabanta cikin kwanaki uku kan tsarin haraji ga yan kasashen waje
- Kungiyar New Kosol Welfare Initiative ta nemi dakatar da sabon tsarin haraji na (EEL) don kare tattalin arzikin kasa da samar da kuɗin shiga
- Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce ya zama dole gwamnati ta dakatar da aiwatar da tsarin harajin har sai an gama sauraren karar da ake yi a kotu
- Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da ce-ce-ku-ce kan sabon kudirin haraji wanda gwamnonin Arewa da shugabanninta ke kalubalanta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Ministocin tarayya biyu su gurfana a gabanta nan da kwanaki uku kacal.

Kara karanta wannan
Harin sojoji: Gwamna ya jajanta, ya yaba wa jami'an tsaro kan tarwatsa yan bindiga
Daga cikin Ministocin akwai na cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, da na Shari'a, Lateef Fagbemi kan haraji game da yan kasashen waje.

Source: Twitter
Kotu ta ba Ministocin Tinubu guda 2 umarni
Premium Times ta ce Kotun ta bukaci Ministocin su bayyana dalilin da ya sa bai kamata a dakatar da sabon tsarin haraji na Expatriate Employment Levy (EEL) ba.
Mai shari’a, Inyang Ekwo ya bayar da wannan umarni ne bayan lauyan masu kara ya shigar da korafi kan bukatar gaggawa a kotun game da harajin.
Kungiyar New Kosol Welfare Initiative ta nemi a dakatar da aiwatar da tsarin haraji, tana mai bayyana shi a matsayin wanda zai takura tattalin arziki.
Yadda tsarin harajin zai yi aiki kan 'yan kasar waje
A cewar kungiyar, Gwamnatin Tarayya ta sanar da wannan sabon tsarin haraji ne a ranar 27 ga Fabrairu, 2024, tare da karin dokokin hukunta waɗanda suka kauce.
An bayyana cewa duk kamfanin da ya dauki kwararru yan kasashen waje zai biya harajin $15,000 ko $10,000, gwargwadon matsayinsu a aiki.

Kara karanta wannan
Laifuffukan yanar gizo: Tinubu da gwamnoni 36 sun shiga matsala, an jero zarge zarge kansu
Kungiyar ta kuma bayyana cewa rashin bin dokokin tsarin zai jawo tara ko kuma hukunci mai tsauri, har da daurin shekaru biyar a gidan yari.
Yaushe za a cigaba da zama kan shari'ar?
Masu shigar da kara suka ce sabon tsarin harajin zai kawo cikas ga cigaban tattalin arzikin kasa saboda yadda yake da tsauri.
Mai shari’a Ekwo ya umarci wadanda ake kara su nuna dalilin da ya sa bai kamata kotu ta amince da bukatun masu kara ba.
Alkalin kotun ya dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 16 ga Janairun 2025 domin sake zama kan matsalar, cewar The Guardian.
Legit Hausa ta yi magana da masanin tattalin arziki
Bello Lamido ya ce haraji shi ne ginshikin ci gaban kowace kasa a duniya.
Sai dai ya ce dole ya kasance ba a tsauwalawa al'umma ta yadda ba za a samu matsala ba.
"Duk inda haraji ya ke yana da matukar muhimmanci matukar ba a sanya yadda zai gagari mutane ko kuma kamfanoni ba."
- Bello Lamido
Malamin ya ce kasashe da yawa sun dogara da haraji daga mutanen kasa saboda ayyukan raya kasa.
Kudirin haraji: Tinubu ya fara lallaba manyan Arewa
Kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya fara tura wakilai zuwa wurin manyan Arewa da wasu yan siyasa don samun goyon baya kan kudirin gyaran haraji.
Gwamnonin Arewa sun jaddada matsayinsu na kin amincewa da kudirin gyaran haraji duk da kokarin Tinubu wanda har yanzu ake ta faman surutu a kai.
Shugaban gwamnonin Arewa, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya ce ba za su janye matsayinsu ba sai an sake nazarin kudirin gyaran harajin da ake magana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
