Abba Ya Dauko Yaki da Talauci Gadan Gadan, Ya Raba Jarin Naira Biliyan 2.1 a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya raba tallafin Naira biliyan 2.1 ga mata 41,600 domin bunkasa ƙananan sana’o’i da tattalin arziki
- Bincike ya nuna cewa gwamnatin Kano ta fara wannan shirin a watan Mayun 2024, inda ake ba wa kowace mace N50,000 a duk wata
- Gwamnan Kano ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafa wa mata da matasa domin magance fatara da talauci a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya raba tallafin Naira biliyan 2.1 ga mata 41,600 a cikin watanni tara da suka gabata, a matsayin tallafi domin bunkasa ƙananan sana’o’i.
Shirin, wanda aka fara a watan Mayu na shekarar 2024, yana bayar da N50,000 a duk wata ga kowace daga cikin mata 5,200 da aka zaɓa daga ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sannusi Bature Dawakin Tofa ne ya fitar da sanarwa kan shirin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bayyana cewa tallafin yana cikin tsare-tsaren gwamnatin sa na yaki da talauci da bunkasa tattalin arzikin jihar Kano.
Manufar shirin tallafin mata a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana shirin a matsayin muhimmin mataki wajen magance talauci da bunkasa tattalin arziki.
A lokacin da yake kaddamar da wani sabon rukuni na mata 5,200 da suka ci gajiyar shirin a ranar Laraba a fadar gwamnatin jihar Kano, gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da shirin duk wata.
Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa daga lokacin da aka fara shirin, mata 41,600 sun ci gajiyarsa.
Abba ya yi kira ga mata a jihar Kano
Abba Kabir Yusuf ya bukaci matan da aka basu tallafin da su yi amfani da kudin wajen habaka ƙananan sana’o’insu.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin sa tana da niyyar fitar da dubban al’ummar jihar daga kangin talauci ta hanyar shirye-shirye irin wannan.
Shirin tallafin matasan jihar Kano
A yayin da yake magana kan tallafin matasa, Gwamna Yusuf ya ce ana horas da matasa masu yawa a cibiyoyin koyon sana’o’i guda 26 da ke jihar Kano.
Ya bayyana cewa wannan horo yana da nufin ba matasan damar yin amfani da basirarsu wajen dogaro da kai tare da habaka tattalin arziki a jihar.
Goyon bayan ma’aikatar zuba jari ta Kano
Kwamishinan Ma’aikatar Zuba Jari ta Kano, Shehu Wada Sagagi, ya bayyana cewa ma’aikatarsa za ta yi kokari domin yin rijistar matan a matsayin ƙungiyoyin haɗin gwiwa.
Sagagi ya ce wannan mataki zai taimaka wajen inganta harkokin kasuwancinsu da samar da ƙarin dama ta hanyar samun tallafi daga bankuna da hukumomin zuba jari.
Wasu daga cikin matan da suka ci gajiyar shirin sun bayyana godiyarsu ga gwamna Abba Kabir Yusuf saboda wannan tallafi, wanda suka ce zai canja rayuwarsu da na iyalansu.
Abba zai raba tallafin ambaliya a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta ware kudi domin rabawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2024.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai raba kimamin Naira biliyan 3 domin rage musu radadin rayuwa bayan shiga matsalar ambaliyar ruwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng