Gwamna Zulum Ya Halarci Taron MNJTF a Ƙasar Waje, Ya ba Iyalan Sojoji Tallafin N300m
- Gwamna Babagana Umara Zulum ya halarci taron rundunar sojin haɗin guiwa watau MNJTF a birnin N'Djamena a kasar Chadi
- Gwamnan Borno ya ba da tallafin Naira miliyan 300 ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a yakin da ake yi da ƴan ta'adda
- Zulum ya yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa ɗaukar matsalar tsaro da muhimmanci musamman a Arewa maso Gabas
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bayar da tallafin Naira miliyan 300 ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a yakin da ake yi da 'yan Boko Haram.
Gwamna Zulum ya sanar da haka ne a taron karrama sojojin da suka mutu a fagen fama na rundunar sojin haɗin guiwa MNJTF a birnin N'Djamena na Jamhuriyar Chadi.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa taron ya gudana a ranar Laraba, inda aka yabawa sadaukarwar sojojin da suka rasa rayukansu wajen kare al'umma daga 'yan ta'adda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Zulum ya faɗi amfanin tallafin
Zulum ya bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka matuka wajen rage radadin da iyalan wadanda suka rasa rayukansu ke fuskanta.
Ya kara da cewa za a raba kudaden ne ta hannun gidauniyar da aka kafa ta musamman domin girmama jaruman da suka rasa rayukansu da kuma tallafawa iyalansu da suka bari.
Yadda za a rabawa iyalan sojoji tallafi
"Babban Hafsan Tsaron Ƙasa ya kafa wata gidauniya da za ta kula da walwalar iyalan sojojin da suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka ji rauni a fagen daga.
“Babu abin da za mu iya yi masu na alheri fiye da wannan; sun sadaukar da rayukansu ta hanyar biyan farashin da ya fi komai girma.
"Za mu ci gaba da tallafa musu. Na ji daɗi cewa an kafa irin wannan gidauniya, idan akwai wata jiha a Najeriya da ya dace ta ba gidauniyar tallafi, to Borno ce.”
- Babagana Zulum.
Ya ce irin wannan tallafi na gwamnati zai kara karfafa gwiwar dakarun sojin Najeriya da sauran kasashen da ke aiki tare domin yaki da 'yan ta’adda.
Ta'addanci ya ragu a tafkin Chadi
Gwamna Zulum ya jaddada cewa, duk da irin kalubalen da ake fuskanta a yankin Arewa maso Gabas, an samu raguwar ayyukan ta'addanci.
Ya kuma yi kira ga sojoji da sauran hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kawo karshen sauran ragowar 'yan Boko Haram da ke cin karensu babu babbaka, musamman a yankin Tafkin Chadi.
Zulum ya nuna godiya ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa jajircewarsa wajen yaki da matsalar tsaro musamman a yankin Arewa maso Gabas.
Yadda aka fara taron da Zulum ya halarta
Wannan taro na rundunar sojin haɗin guiwa an fara shi ne a shekarar 2017, kuma yana da nufin karrama sojojin da suka yi kwanta dama a fagen fama.
Taron yana ƙara yabawa dakarun soji da kwamandojinsu bisa ƙoƙarin da suke wajen ganin an kakkaɓe 'yan ta’adda a kasashen da ke kewaye da Tafkin Chadi, kamar Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru.
Shugaba Tinubu ya yi alhinin kisan sojoji
Kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi jimami da alhinin kisan sojoji shida a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Shugaba Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da rundunar sojojin sannan ya yaba da martanin da dakarun suka mayar a lokacin harin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng