An Kama Mai Bautar Gumaka da Ya Wulakanta Kur'ani, Ya Banka Masa Wuta

An Kama Mai Bautar Gumaka da Ya Wulakanta Kur'ani, Ya Banka Masa Wuta

  • Jami’an tsaro sun cafke wani fitaccen mabiyin addinin gargajiya, Balogun Aaba, bisa zargin ƙona Al-Kur’ani mai girma
  • An ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan wallafa wani bidiyo da ya nuna shi yana kona Kur'anin kuma aka shigar da shi kara
  • Wani malamin addini da ya zanta da Legit ya ba Musulmai shawara a kan abin da ya kamata su rika yi idan aka samu yanayi irin wannan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Jami’an tsaro sun cafke wani fitaccen mabiyin addinin gargajiya mai suna Balogun Aaba, wanda aka fi sani da Odofin na Iseyin, bisa zargin ƙona Al-Kur’ani.

Lamari ya fusata mabiyan addinin Musulunci a jihar, inda suka yi kira ga hukuma da ta dauki matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Abba ya dauko yaki da talauci gadan gadan, ya raba jarin Naira biliyan 2.1 a Kano

Aaro Yoruba
An kama wanda ya kona Al-Kur'ani a Oyo. Hoto: Balogun Aaba, Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An kama Aaba ne a ranar Laraba, 8 ga Janairu, 2025, bayan wallafa bidiyon da ya nuna yana ƙona Al-Qur’ani a shafinsa na sada zumunta, Oro Yoruba TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama Aaba kan kona zargin Kur'ani

Legit ta ruwaito cewa wasu mabiyan addinin Musulunci sun rubuta ƙorafi ga hukumomin tsaro kan bidiyon da Aaba ya wallafa.

Bidiyon, wanda aka wallafa a ranar 23 ga Disamba, 2024, ya nuna Aaba yana ƙona Al-Qur’ani, wanda hakan ya haifar da rashin jin dadi tsakanin mabiyan addinai.

Wani jagoran mabiyan addinin gargajiya, Abdulazeez Adegbola, wanda aka fi sani da Tani Olohun,ya tabbatar da kamun Aaba.

Tani Olohun ya wallafa a Facebook cewa an dauki Aaba zuwa Eleyele, Ibadan, domin gudanar da bincike.

Ra'ayoyin jama'a a kafafen intanet

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke Allah-wadai da aikin, yayin da wasu ke kira da a girmama addinai daban-daban.

Kara karanta wannan

Wani shahararren ɗan sandan Najeriya ya Musulunta, ya canja suna zuwa Muhammad

Wasu na ganin irin wannan aiki na iya haifar da rikici tsakanin addinai, yayin da wasu ke cewa ya dace mabiyan addinai su guji duk wani abu da zai tayar da hankali a cikin al’umma.

Duk da haka, Tani Olohun ya bayyana cewa akwai matsaloli da mabiyan Isese ke fuskanta, yana mai kira ga Yarabawa su tashi tsaye domin kare al’adunsu.

Bukatar zaman lafiya a Oyo

Masana da shugabannin al’umma sun yi kira ga mabiyan addinai daban-daban da su yi taka-tsantsan wajen mu’amala da juna.

Sun bayyana cewa ya kamata kowa ya girmama addinin juna domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.

A yanzu haka dai ana gudanar da bincike domin gano gaskiyar al’amari da kuma daukar matakin da ya dace.

Muhimmancin girmama addinai

Lamari ya kara jaddada muhimmancin zaman lafiya da girmama bambancin addinai a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan tsaro yayin da sojoji ke kokarin cafke Turji

Masu sharhi sun yi kira ga hukumomi da su tabbatar da adalci a yayin bincike, tare da gujewa duk wani abu da zai kara tayar da hankali a cikin al’umma.

Legit ta tattauna da malamin addini

Wani malamin addini, Kamil Muhammad ya bayyanawa Legit cewa matakin da aka dauka na sanar da jami'an tsaro shi ne mafi dacewa.

Ustaz Kamil ya bayyaana cewa a ko da yaushe akwai bukatar kwantar da hankali idan aka samu yanayi irin wannan.

Malamin ya ce:

"Idan da sun dauki doka a hannu, da sun jawo wa Musulunci bakin jini duk da cewa kona Kur'ani aka yi. Mutane za su yi wa Musulunci mummunar fassara a dalilinsu"

Yan sanda sun kama makamai

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun cafke 'yan bindiga da tarin makamai a wani rukunin samame da suka kai a jihohi.

Rahoton Legit ya nuna cewa jami'an tsaron sun gudanar da samamen ne a jihohin Benue, Nasarawa da Bayelsa a Kudancin kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng