An Yi Arangama tsakanin Yan Ta'adda, An Hallaka Hatsabibin Dan Bindiga yayin Rigimar

An Yi Arangama tsakanin Yan Ta'adda, An Hallaka Hatsabibin Dan Bindiga yayin Rigimar

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an hallaka sanannen shugaban 'yan bindiga, Kachalla Dogo Isah a wata arangama da wata kungiyar tubabbun 'yan bindiga
  • Rikicin ya faru ne a Dajin Kachia a ranar 7 ga Janairu, 2025, yayin da Dogo Isah ya yi yunkurin kwace shanu daga sansanin Kachalla Musa a jihar Kaduna
  • Kachalla Musa, tsohon shugaban 'yan bindiga da ya tuba, ya jagoranci rikicin da ya yi sanadin mutuwar Dogo Isah tare da wasu daga cikin 'yan kungiyarsa
  • An tabbatar da cewa Kachalla Musa ya tuba daga ayyukan ta'addanci bayan karbar tayin gwamnati da kuma ajiye makamansa domin samun zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kachia, Kaduna - An tabbatar da mutuwar wani sanannen shugaban 'yan bindiga a Kaduna, Kachalla Dogo Isah a wata arangama da wata kungiyar yan ta'adda.

Rahotanni sun ce rikicin ya faru ne a Dajin Kachia a ranar 7 ga Janairun 2025, yayin da Dogo Isah da 'yan kungiyarsa suka kai farmaki a sansanin Kachalla Musa.

Kara karanta wannan

Fadan kabilanci ya yi sanadin rasa rayukan mutane 11 a Jigawa, an fadi silar rikicin

Rigima tsakanin yan bindiga ta yi ajalin hatsabibin dan bindiga
An yi rigima tsakanin yan bindiga wanda ya yi sanadin hallaka Dogo Isah a Kaduna. Hoto: Legit.
Asali: Original

An hallaka fitaccen dan bindiga a Kaduna

Zagazola Makama ya ce Dogo Isah ya yi yunkurin kwace shanu daga sansanin tsofaffin 'yan bindiga karkashin jagorancin Kachalla Musa wadanda suka tuba kwanaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da cewa Kachalla Musa yanzu ya kasance mai goyon bayan zaman lafiya tare da barin ayyukan ta'addanci bayan yarjejeniya da gwamnati.

Rikicin ya rikide zuwa harin yan bindiga mai tsanani, wanda ya yi sanadin mutuwar Dogo Isah tare da wasu biyu daga cikin 'yan kungiyarsa.

Hare-haren da Kachalla Dogo ya kai a Kaduna

Kachalla Dogo Isah ya shahara wajen ta’addanci a yankunan Kachia da Kajuru, ya jagoranci hare-hare da dama kan al’umma da ya yi sanadin rasa rayuka.

Dogo Isah shi ne dan uwan Tukur Sharme, wani babban shugaban 'yan bindiga, wanda aka kashe a rikici irin wannan a watan Satumbar 2024, cewar Daily Post.

Kachalla Musa ya shiga tsarin zaman lafiya tare da goyon bayan gwamnati da hukumomin tsaro a jihar Kaduna bayan taron zaman lafiya a kauyen Tsohon Gaya da ke karamar hukumar Chikun.

Kara karanta wannan

Faransa ta yi magana kan zargin hada kai da Najeriya ta yamutsa Nijar

Gwamnati tana ba yan bindiga damar tuba

An gano cewa gwamnatin Kaduna ta na ba tsofaffin 'yan bindiga damar yin sulhu, amma Dogo Isah ya ki karbar wannan tayin.

Dogo Isah ya jagoranci hare-haren da suka hada da kashe sojoji da jami'an tsaro a shekarun baya, ciki har da hari kan sojojin ruwa a Kujama.

Mutuwar Dogo Isah ta kasance babbar nasara a yaki da ta’addanci, amma ta haifar da damuwa tsakanin kungiyar tubabbun yan ta'adda ta Kachalla Musa.

Yan bindiga sun buga ta'asa a Kaduna

Kun ji cewa wasu yan bindiga dauke da makamai sun yi ta'asa a jihar Kaduna ta hanyar sace mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Yan bindigan sun bi dare yayin da suka sace mutane 16 a kauyen Mararraba Mazuga da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Wasu daga cikin mutanen da aƙa sace sun tsere yayin da aka sako wasu domin su zo su karɓo kuɗaɗen fansan ragowar waɗanda ke tsare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.