"Ba Talaka ba ne a Gabansu," Hadimin Tinubu Ya Faɗi Dalilin Gwamnoni na Sukar Kudirin Haraji

"Ba Talaka ba ne a Gabansu," Hadimin Tinubu Ya Faɗi Dalilin Gwamnoni na Sukar Kudirin Haraji

  • Hadimin shugaban ƙasa ya ce gwamnonin da ke adawa da kudirin haraji abin da za su samu ne a gabansu ba jin daɗin talakawa ba
  • Daniel Bwala ya ce galibin gwamnonin danuwarsa idan kudirin ya zama doka za a rage masu kason kuɗin da ake turawa jihohinsu
  • Ya ce gwamnatin tarayya ba za ta tsaya ɓata lokaci kan ra'ayoyin gwamnonin ba domin sabon tsarin zai inganta rayuwar duka ƴan Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala ya ce gwamnonin da ke adawa da kudirin haraji ba su damu da walwalar ƴan Najeriya ba.

Bwala ya yi ikirarin cewa duk gwamnan da ya fito ya soki kudirin sauya fasalin harajin damuwarsa kawai kuɗin da za a tattara, ba ruwansa da jin daɗin jama'a.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta amince da ƙara kuɗin kiran waya da sayen data a Najeriya

Daniel Bwala.
Hadimin Tinubu ya caccaki gwamnonjn da ke adawa da kudirin haraji Hoto: @bwaladaniel
Asali: Twitter

Hadimin shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels tv a farkon makon nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda kudirin haraji ya tayar da ƙura

Idan ba ku manta ba, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudirori huɗu a gaban Majalisar Tarayya na gyara tsarin tattara haraji da kasafta shi.

Babban abin da ya ja hankali tare da tada ƙura a tsakanin ƴan Najeriya shi ne tanadin da aka yi a sabon kudirin dangane da rabon harajin kayayyaki watau VAT.

Gwamnonin Arewa sun fito sun nuna adawarsu da kudirin, suka ce idan ya zama doka wasu jihohi ba za su iya biyan ma'aikata albashi ba.

Da yake martani kan sukar da ake wa kudirin, Bwala ya ce sabon tsarin harajin ba batu ba ne na yanki, kamar yadda The Cable ta ruwaito shi.

Ba gwamnonin Arewa kaɗai ke sukar tsarin ba

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya gargadi kwamishinoni, ya fadi abin da ba zai lamunta ba

Ya ce muhawarar da ake yi kan kudirin wani ɓangare ne ja matakan yin doka kamar yadda yake ƙunshe a kundin tsarin mulkin Najeriya.

Daniel Bwala ya ce:

"Akwai wasu gwamnonin Najeriya waɗanda ba ’yan Arewa ba ne su ma suna adawa da kudirin, wasu daga cikinsu da ba su ce komai ba amma sun bayyana ra'ayoyinsu."
'"Ba gudu ba ja da baya game da kudurin haraji kuma Majalisa za ta amince da shi, mu manta da wani batun Arewa ko Kudu, gwamnonin jihohin da kason su zai ragu ne ke adawa da shi.
"Su na da yawa ba wai gwamnonin Arewa ne kaɗai ba, su dai gwamnonin Arewa ba su ɓoye matsayarsu ba, sun fito sun yi magana, amma ba su kaɗai ba ne suke adawa da tsarin.

Kudirin haraji: Abin da gwamnoni ke tunani

Daniel Bwala ya kara da cewa tunanin gwamnonin kawai za a rage kuɗin da ake tura masu idan kudirin ya zama doka amma ba su tunanin ƴan Najeeiya sama da miliyan 200.

Kara karanta wannan

Hadimin shugaban ƙasa ya faɗi jiha 1 da kudirin harajin Tinubu zai fi yi wa illa

Ya ce idan ka duba abubuwan da ke kunshe a kudirin zaka ga zai amfani dukkan ƴan Najeriya ne ba wai iya gwamnoni 36 ko 37 duk da ministan Abuja ba.

Kwamitin haraji ya musanta ikirarin dattawan Arewa

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kwamitin gyaran haraji na shugaban ƙasa ta musanta zargin da dattawan Arewa suke yi mata.

Taiwo Oyedele ya bayyana cewa sai da suka zauna da malamam addini da masi ruwa da tsaki a Arewa kan batun canza fasalin haraji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262