Jami'an Tsaro Sun Gwabza da 'Yan Bindiga, Sun Kubutar da Mutanen da Suka Sace

Jami'an Tsaro Sun Gwabza da 'Yan Bindiga, Sun Kubutar da Mutanen da Suka Sace

  • Mugun nufin ƴan bindiga na yin garkuwa da wasu fasinjoji ya gamu da cikas a jihar Sokoto da ke fama da matsalar tsaro
  • Tawagar jami'an tsaro na haɗin gwiwa sun yi nasarar daƙile harin tare da kuɓutar da mutanen da aka nemi a dauke
  • Mataimakin gwamnan Sokoto wanda ya karɓi mutanen da aka ceto, ya yabawa tawagar jami'an tsaron kan namijin ƙoƙarin da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Tawagar haɗin gwiwa ta ƴan sanda tare da jami'an rundunar tsaron Sokoto, ta yi nasarar daƙile wani harin ƴan bindiga.

Tawagar jami'an tsaron sun daƙile harin na ƴan bindigan ne a kan wata mota mai jigilar fasinjoji a Kwanar Mahalba, kan hanyar Goronyo-Sabon Birni, a ranar Laraba.

Jami'an tsaro sun fatattaki 'yan bindiga a Sokoto
Jami'an tsaro sun dakile harin 'yan bindiga a Sokoto Hoto: @AhmedaliyuSkt, @PoliceNG
Asali: Twitter

A yayin aikin ceton, tawagar jami'an tsaron ta kuɓutar da mutum bakwai daga cikin fasinjoji 13 da ke cikin motar, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Yadda jami'in tsaro ya rasa ransa bayan ceto mutanen da aka sace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutum biyar daga cikin fasinjojin sun tsere cikin daji, amma ɗaya daga cikinsu ya rasa ransa sakamakon harbin da ƴan bindiga suka yi masa.

Gwamnati ta yabawa jami'an tsaro

Da yake karɓar mutanen da aka ceto, mataimakin mwamnan jihar Sokoto, Alhaji Idris Mohammed Gobir, ya jinjinawa tawagar haɗin gwiwar bisa namijin ƙoƙarin da suka yi, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Alhaji Idris Mohammed Gobir ya nuna godiyarsa kan cewa a cikin kwanaki huɗu da suka gabata, tawagar haɗin gwiwar ta ceto mutum 63 daga hannun ƴan bindiga.

"Alƙaluma sun nuna cewa an ceto mutum 24 a ranar Lahadi, mutum 39 a ranar Litinin, sannan mutum bakwai a ranar Laraba."
"Ina tabbatar muku cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon baya da tallafin da ake buƙata ga tawagar hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga a jihar."
“Gwamna Ahmed Aliyu ya bayar da umarnin cewa duk abin da ake buƙata don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar, a samar da shi ba tare da wani jinkiri ba."

Kara karanta wannan

Barazanar tashin bam: Gwamnatin Neja ta aika da muhimmin gargadi ga manoma

- Alhaji Idris Mohammed Gobir

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya suna ƙara ƙaimi wajen yaƙar ayyukan ƴan ta’addan Lakurawa.

Yadda ƴan bindiga suka so sace fasinjoji

Da yake magana a madadin mutanen da aka ceto, Malam Umar Isa Magajin Gatarawa ya ce suna tafiya ne daga Isa zuwa Sokoto lokacin da ƴan bindiga suka tare hanya a kan Kwanar Mahalba.

Ya ce lokacin da direban motar ya yi ƙoƙarin tserewa, sai ƴan bindigan suka harbi tayoyin motar.

Malam Umar ya ce yayin da fasinjojin suka fara tserewa zuwa cikin daji don tsira, sai tawagar haɗin gwiwar da ke sintiri ta isa wurin, suka tilastawa ƴan bindigan tserewa bayan musayar wuta.

Sai dai ya bayyana cewa ɗaya daga cikin fasinjojin ya rasa ransa sakamakon harbin bindiga.

Jami'in tsaro ya rasa ransa a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa an shiga jimami a jihar Sokoto bayan wani jami'in rundunar tsaron Sokoto ya rasa ransa har lahira.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi abin da za ta yi wa wadanda gobarar kasuwar Kara ta shafa

Jami'in tsaron dai ya harbi kansa ne bisa kuskure bayan sun dawo daga ceto mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng