Fadan Kabilanci Ya Yi Sanadin Rasa Rayukan Mutane 11 a Jigawa, an Fadi Silar Rikicin

Fadan Kabilanci Ya Yi Sanadin Rasa Rayukan Mutane 11 a Jigawa, an Fadi Silar Rikicin

  • Rahotanni sun ce akalla mutane 11 sun rasa rayukansu yayin da aka kona gidaje 31 a Gululu, a Jahun da Miga a jihar Jigawa
  • Wani dattijon Bafulatani, Sulaiman Abubakar Jahun, ya bayyana yadda ya rasa yaransa 5 yayin rikicin ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi
  • Hukumar ba da agaji ta SEMA ta bada tallafi ga wadanda abin ya shafa, ciki har da shinkafa da kudi, tare da alkawarin tabbatar da zaman lafiya
  • Kwamishinan yan sanda a Jigawa, AT Abdullahi ya ba yan jihar tabbacin zakulo wadanda suka aikata laifuffukan tare da daukar mataki kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jahun, Jigawa - An shiga wani irin yanayi bayan tabbatar da cewa mutane 11 ne suka rasa rayukansu yayin wani rikici a jihar Jigawa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan rasa rayuka, an kona gidaje 31 a kauyen Gululu na Jahun kan rikicin Fulani da Hausawa a Jigawa.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan tsaro yayin da sojoji ke kokarin cafke Turji

An rasa rayuka a Jigawa kan rikicin kabilanci
Fadan kabilanci ya yi sanadin rasa rayukan mutane 11 a Jigawa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Dattijon Bafulatani ya fadi rashin da ya yi

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan lamarin ya faru ranar Juma’ar da ta gabata, wanda ya jefa jama’a cikin tsoro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani daga cikin dattawan Fulani, Sulaiman Abubakar Jahun, ya bayyana yadda ya rasa yara 5, yana mai cewa ba su da hannu cikin rikicin da ya faru.

“Ina gida ne sai aka zo aka sanar da ni rikici ya barke tsakanin Hausawa da Fulani, na iske abin takaici da kisan gilla.”

- Sulaiman Abubakar

Wasu mazauna Jahun sun roki gwamnati alfarma

Abubakar ya roki gwamnati ta taimaka masa, ganin cewa yanzu shi ke kula da jikokinsa 18 bayan rasa yaransa.

Wani wanda ya rasa dansa, Amadu Garba Jahun, ya ce ba za su rama wannan rikici ba, amma sun bar komai hannun Allah, cewar Tribune.

“Ba muna son daukar doka a hannu ba, abin da muke so shi ne gwamnati ta tabbatar mana da adalci da zaman lafiya.”

Kara karanta wannan

'Na san za a zage ni': Tinubu ya fadi shirin da yake yi wa Najeriya

- Amadu Garba

Hukumar SEMA ta ba da agajin na musamman

Hukumar ba da agaji ta SEMA ta bada gudummawar buhunan shinkafa 25 da Naira dubu 500 ga iyalan da abin ya shafa domin rage musu radadi.

Shugaban SEMA, Dr. Haruna Mairiga, ya ce rikicin ya samo asali ne daga sata, wanda ya kai ga tashin hankali mai muni.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, CP AT Abdullahi, ya ce gwamnati ta kafa kwamiti don magance rikici, tare da kama masu hannu dumu-dumu.

Kwamishinan ya bukaci al'umma su kwantar da hankulansu ba tare da daukar doka a hannu ba inda ya yi alkawarin zakulo wadanda ska aikata laifin.

Amarya ta saka guba a abincin angwaye

A baya, kun ji cewa rahotanni na nuni da cewa wani aure a Jihar Jigawa ya koma zaman makoki bayan zargin amarya da sanya guba a abincin ango.

Bayanan 'yan sanda sun tabbatar da cewa an kwantar da mutane a asibiti yayin da daya daga cikin abokan ango ya rasa ransa.

Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta kama amarya da wata mace domin bincike da kuma daukar mataki na gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.