Kwana Ya Kare: Yadda Jami'in Tsaro Ya Rasa Ransa bayan Ceto Mutanen da Aka Sace

Kwana Ya Kare: Yadda Jami'in Tsaro Ya Rasa Ransa bayan Ceto Mutanen da Aka Sace

  • An shiga jimami a jihar Sokoto bayan wani jami'in rundunar tsaro a riga mu gidan gaskiya bayan tsautsayi ya ritsa da shi
  • Jami'in tsaron ya rasa ransa ne lokacin da ya harbi kansa bisa kuskure bayan an ceto wasu mutanen da ƴan bindiga suka sace
  • Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar 8 ga watan Janairu 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Wani jami’in rundunar tsaron jihar Sokoto (wanda ba a bayyana sunansa ba) ya harbi kansa bisa kuskure har lahira.

Jami'in tsaron ya harbi kan nasa ne bisa kuskure jim kaɗan bayan halartar wani aikin haɗin gwiwa da ya kai ga ceto mutane 66 da aka sace a jihar.

Jami'in tsaro ya rasu a Sokoto
Jami'in tsaro ya harbi kansa a Sokoto Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa farmakin haɗin gwiwar wanda sojoji suka jagoranta, an gudanar da shi ne a ranar Litinin a dajin Tidibali da ke gabashin jihar.

Kara karanta wannan

Barazanar tashin bam: Gwamnatin Neja ta aika da muhimmin gargadi ga manoma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa jami’in rundunar tsaron ya rasa ransa ne sakamakon harbin bindiga bisa kuskure.

“Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan sun dawo sansaninsu daga aikin ceto. Yana tare da bindigarsa, sai ta tashi bisa kuskure ta harbe shi, sai ya rasu nan take."

- Kanal Ahmed Usman.

Jami'an tsaro ragargazar ƴan bindiga

A cewarsa, an samu gagarumar nasara a farmakin haɗin guiwar da ake gudanarwa wanda gwamnatin jihar ke ɗaukar nauyi don murƙushe ƴan bindiga.

Ya ce wannan aiki yana daga cikin matakan da gwamnati ta ɗauka don tabbatar da tsaro da kawar da masu aikata laifi daga jihar Sokoto.

"Ya zuwa yanzu, nasarorin da aka samu sun haɗa da ceto mutane 66 da aka yi garkuwa da su, tare da kashe ƴan bindiga da dama a yayin farmakin."

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Tsohon sakataren gwamnatin jiha a Najeriya ya rasu

"Wannan nasara tana nuna jajircewar gwamnati da rundunonin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya."

- Kanal Ahmed Usman

Gwamnati za ta ci ga yaƙar ƴan bindiga

Ya kuma ƙara da cewa yaƙin ba zai tsaya ba, domin gwamnati tana da burin kawar da duk masu aikata laifi daga cikin jihar.

Kanal Ahmed Usman ya ce za a ci gaba da kai hare-hare a maɓoyar ƴan bindiga domin murƙushe su gaba ɗaya.

Wani mazaunin ƙaramar hukumar Isa ya tabbatar da cewa mutanen da aka ceto daga hannun ƴan bindigar an kawo su zuwa garin Isa.

Wannan nasara ta farantawa al’ummar yankin rai, inda suke fatan samun zaman lafiya da dawowar walwala a yankunansu.

A cewar majiyoyin tsaro, wannan yaƙin wani muhimmin mataki ne na kawar da ƴan bindiga da maida da jihar Sokoto ta koma wurin da ake samun zaman lafiya.

Jirgin ruwa ya kife a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu wani hatsarin jirgin ruwa da ya ritsa da fasinjoji a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Sarki a Najeriya ya gamu mummunan hatsari, Allah ya yi masa rasuwa

Hatsarin jirgin ruwan wanda ya auku a gundumar Dundaye ya yi sanadiyyar rasuwar wani dattijo mai shekara 60 da haihuwa a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng