Hafsan Tsaro Ya 'Gano' Masu Taimakon Ta'addanci, Ya Nemi Alfarmar Majalisar Dinkin Duniya
- Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta yi binciken kudaden da ake taimaka wa Boko Haram da ta'addanci
- Janar Musa ya bayyana cewa fiye da mayakan Boko Haram 120,000 sun mika wuya, kuma da dama suna da makudan kudaden ketare wanda ya jawo zarge-zarge
- Ya nuna alamar akwai makarkashiya ta kasa da kasa da ke kara rura wutar ta’addanci a Najeriya musamman a yankin Arewacin Najeriya baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya koka kan tallafin kudade da goyon baya daga ketare da ke taimaka wa Boko Haram.
Janar Musa ya bayyana cewa wannan goyon baya ya sa ’yan ta’addan suka lalata kasar tsawon shekaru fiye da goma sha biyar inda ya ruguza tattalin arzikin yankin.
Hafsan tsaro ya nemi taimakon Majalisar Dinkin Duniya
Janar Musa ya yi wannan furuci ne yayin wata hira da ya yi da Al Jazeera, da wakilinmu ya bibiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hafsan tsaron ya roki Majalisar Dinkin Duniya ta binciki asalin kudin da ’yan ta’addan suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu da kuma irin karfin da suke da shi wanda ke neman fin na sojoji.
“Mun tattauna da al’ummomin duniya, mu gano daga ina kudin ke fitowa, fiye da 120,000 sun mika wuya."
“Majalisar Dinkin Duniya ce kadai za ta iya gano irin wadannan kudi, ba mu da iko a kai.”
- Janar Christopher Musa
Yawan wadanda suka mika wuya ga sojoji
Janar Christopher Musa ya kara da cewa yawancin wadanda suka mika wuya 120,000 suna da makudan kudin ketare, ya tambaya inda ya koka kan inda suka same su.
Ya ce wannan al’amari ya shafi kwararar kudade daga kasashen duniya, wanda Najeriya ba za ta iya magancewa ita kadai ba, cewar jaridar Leadership.
“Wata kila akwai makarkashiya ta kasa da kasa—waye ya sani?, “Ta yaya suka iya tsayawa tsawon shekaru goma sha biyar?”
- Cewar Janar Musa
Janar Christopher Musa ya bayyana wannan tambayar a matsayin abin da kowa ya kamata ya yi tunani a kai domin samun mafita ga wannan matsalar.
Ya ce abin takaici ne yadda sojoji kullum ke ƙoƙarinsu amma lamarin sai kara ta'azzara yake yi saboda zargin taimaka musu da ake yi daga ketare.
Nasarar da sojoji suka samu kan yan ta'adda
A baya, kun ji cewa Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi ƙarin haske kan harin da mayaƙan ISWAP suka yi yunkurin kai wa sansanin sojoji a jihar Borno.
Kakakin DHQ na ƙasa, Janar Edward Buba ya ce sojoji sun yi nasarar daƙile ƴan ta'addan tun kafin su ida nufinsu a sansanin da ke Sabon Gari.
Buba ya tabbatar da cewa an kashe ƴan ta'adda 34, dakarun soji shida sun rasa ransu yayin musayar wuta da maharan a yankin da ke yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng