Gwamnan Kano Ya Shiga Jimami, Hadiminsa Ya Rasu Awanni bayan Nadinsa
- Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rashin Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure a matsayin babban rashi
- An naɗa Injiniya Bunkure a matsayin mai bai wa gwamna shawara kan ayyuka kwana ɗaya kafin ya koma ga Allah SWT
- Tsohon gamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da sauran jiga-jigai na siyasa na ci gaba da jimaminsa da mika ta'aziyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya shiga jimami da damuwa bayan rasuwar daya daga cikin sababbin hadiman da ya nada.
Gwamna Abba Gida Gida ya naɗa Ahmad Ishaq Bunkure, a matsayin mashawarcinsa na musamman kan harkokin ayyuka a ranar Talata.
A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook, Injiniya Bunkure ya rasu a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin gwamnan ya rasu ne a kasar Masar inda ake kula da lafiyarsa, wanda dama bai kai ga fara aiki a sabon mukamin da Abba ya ba shi ba.
Gwamnan jihar Kano ya mika ta'aziyya
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna alhini bisa rasuwar sabon mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin ayyuka, Ahmad Ishaq Bunkure.
Gwamnan ya bayyana cewa rasuwar Injiniya Bunkure za ta bar babban gibi a gwamnatin Kano, duba da irin jajircewarsa da gudunmawar da ya ke bayarwa.
Sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce:
“Wannan wani lokaci ne mai cike da raɗaɗi gare mu a matsayin gwamnati.
"Injiniya Bunkure ƙwararren masani ne da aka yi tsammanin gudunmawarsa za ta tallafa wajen cika burin cigaban gwamnatarmu. Rashinsa babban raɗaɗi ne a gare mu."
Gwamnan Kano ya yi addu'a ga hadiminsa
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya roki Allah (SWT) da ya sada tsohon hadiminsa, Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure da rahama da mafificiyar Aljannah madaukakiya.
Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure ya rasu jim kaɗan bayan naɗa shi a matsayin mai ba gwamna shawara na kan ayyuka, lamarin da ya girgiza jama'a sosai.
Jama'a na ta'aziyyar rasuwar hadimin gwamnan Kano
Jama'a na ci gaba da ta'aziyyar rashin Injiniya Bunkure daga ciki da wajen Kano, bayan samun labarin rasuwar sabon hadimin gwamna daga bakin gwamnatin Kano.
Sakon ta’aziyya na cigaba da zuwa daga ciki da wajen jihar, ciki har da daga mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da mukarraban gwamnatin jihar.
Gwamna Kano ya nada sababbin kwamishinoni
A baya mun wallafa cewa gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sababbin kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman a gidan gwamnati.
Gwamna Abba ya yi kira ga sababbin shugabannin da su sauke nauyin da aka ɗora musu bisa gaskiya da kishin al’umma, inda ya ce wannan dama ce ta yiwa al’umma hidima.
Daga cikin waɗanda aka rantsar akwai Shehu Wada Shagagi, Ismail Aliyu, da Ibrahim Waiya, inda wamnan ya jaddada mahimmancin haɗin kai don samun ci gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng