Tinubu: Martanin 'Yan Najeriya kan 'Nasihar' Gwamnan Bauchi ga Sheikh Jingir

Tinubu: Martanin 'Yan Najeriya kan 'Nasihar' Gwamnan Bauchi ga Sheikh Jingir

  • Gwamna Bala Mohammed ya shaida wa Sheikh Sani Yahaya Jingir koke-koken da ke damun talakawa domin isarwa ga Bola Tinubu
  • 'Yan Najeriya a kafafen sada zumunta sun yi martani kan yadda gwamnan ya cire tsoro ya fadawa malamin hakikanin halin da ake ciki
  • A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu daga cikin martanin da mutane suka yi kan abin da ya faru tsakanin gwamnan da malamin
  • Wani dan kungiyar Izala, Nafi'u Aliyu ya bayyanawa Legit cewa bai ji dadin abin da gwamnan Bauchi ya fadawa Sheikh Jingir ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - ‘Yan Najeriya sun yi martani kan koke-koken da Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya gabatar wa Sheikh Sani Yahaya Jingir domin isarwa ga shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware biliyoyin Naira kan jiragen shugaban kasa a 2025

Gwamnan ya ce talakawa na shan wahala sakamakon manufofin da gwamnatin Bola Tinubu ke aiwatarwa, ya na mai cewa shugaban kasar ba ya sauraron koke-koken jama’a.

Jingir
'Yan Najeriya sun yabi gwamnan Bauchi kan sakon da ya ba Sheikh Jingir ya isar Tinubu. Hoto: Lawal Mu'azu Bauchi
Asali: Facebook

Jawabin ya zo ne a yayin ziyarar ta’aziyya da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya kai wa Gwamnan Bauchi kamar yadda hadimin gwamnan ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Datti Assalafy: Gwamnan Bauchi bai tsoron mutane

A martaninsa a kafar Facebook, Datti Assalafy ya yaba wa Gwamnan Bauchi bisa isar da koke-koken talakawa ta hanyar Sheikh Jingir.

Datti Assalafy ya ce;

“Kaura ya nuna cewa ba ya tsoron mutane, domin ya bayyana koke-koken jama’a a gaban malamin da aka sani da kusanci da Shugaban kasa Tinubu.”

Assalafy ya kuma bayyana cewa akwai alamar Sheikh Jingir ya nuna rashin jin dadinsa kan koke-koken da gwamnan ya yi.

“Na ga fuskar Sheikh Jingir a turbune, kamar ba ya jin dadin maganar da gwamna Kaura ya yi, kuma wannan ya kara son sa a zuciyata,”

Kara karanta wannan

Tinubu ba ya sauraron kokenmu, Gwamnan Bauchi ya nemi Sheikh Jingir ya shiga tsakani

- Datti Assalafy

Assalafy ya roki Allah ya cigaba da taimakon Gwamnan Bauchi wajen jagorancin jama’a da kawo cigaba ga jiharsa.

"Kauran Bauchi ya yi hikima"

Yasir Haruna Muhammad ya bayyana gwamnan Bauchi a matsayin dan siyasa mai hangen nesa da hikima.

A karkashin haka ne Yasir ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya gane cewa hanya mafi sauki dominn isar da sako ga shugaba Tinubu ita ce ta hannun Sheikh Jingir.

“Kaura ya fahimci cewa Sheikh Jingir yana da karbuwa wajen Shugaba Tinubu da kuma jama’a, domin haka ya yi amfani da wannan dama domin isar da sakonsa,”

- Yasir Haruna Muhammad

Ya kara da cewa dama sun lura cewa Sheikh Jingir ya fara nuna alamun jin takaici kan manufofin gwamnatin Tinubu, domin alkawuran da aka yi ba a cika su bai.

Yasir ya yaba wa Sheikh Jingir da Gwamna bisa kokarin da suke yi domin ganin Najeriya ta samu shugabanci na gari, yana mai rokon Allah ya karbi kokarinsu.

Kara karanta wannan

Zargin barazana: Atiku ya shiga fadan Peter Obi da Tinubu, ya ba da shawara

Muhammad: Allah ya yi wa Kaura albarka

A martanin da ya yi a Facebook, Muhammad A. Adamu ya roki Allah ya yi wa Gwamnan Bauchi albarka bisa jajircewarsa wajen isar da koke-koken jama’a ga Shugaba Tinubu.

“Allah ya yi wa Gwamna Kaura albarka, kuma ya sanya sakon da ya gabatar ya isa ga shugaban kasa.”

- Muhammad A. Adamu

Ya kuma roki Allah ya saka wa Sheikh Jingir da alheri bisa kokarinsa a matsayin jagoran Muslim Muslim a Najeriya.

Martanin jama’a ya nuna yadda talakawa ke neman shugabanni da malamai su yi amfani da tasirinsu wajen isar da koke-koken da ke damun al’umma ga masu madafun iko a Najeriya.

Legit ta tattauna da dan Izala

Wani dan kungiyar Izala, Nafi'u Aliyu ya bayyanawa Legit cewa ya dauki kalaman da gwamnan Bauchi ya yi ga Sheikh Jingir a matsayin cin fuska.

"Ko da zai fada masa hakan, ya kamata ace suna tare su biyu ne. Amma a yadda ya fadi zancen, ya yi magana da duniya ne ba da shugaban malamai kadai ba,"

Kara karanta wannan

Gwamnan da ke sukar kudirin gyaran haraji ya koma goyon bayan tsarin Tinubu

- Nafi'u Aliyu

Dalung ya koka kan mulkin Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Solomon Dalung ya koka kan yadda lamura ke tafiya a karkashin mulkin Bola Tinubu.

Tsohon ministan ya ce lamura ba su tafiya daidai saboda wasu 'yan-ba-ni-na-iya sun kewaye Bola Tinubu kamar yadda aka yi wa shugaba Muhammadu Buhari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng