Sababbin Bayanai Sun Fito kan Ta'asar 'Yan Boko Haram a Sansanin Sojoji da ke Borno

Sababbin Bayanai Sun Fito kan Ta'asar 'Yan Boko Haram a Sansanin Sojoji da ke Borno

  • Ƴan ta'addan Boko Haram sun yi babbar ta'asa bayan sun afkawa sansanin sojoji a jihar Borno a cikin 'yan kwanakin nan
  • Adadin sojojin da suka rasa rayukansu da waɗanda aka nema aka rasa na ci gaba da ƙaruwa kwana huɗu bayan kai harin
  • Majiyoyi daga rundunar sojoji sun bayyana cewa tawagar bincike na ci gaba da gano gawarwakin jami'an da suka rasu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Adadin sojojin da suka rasa ransu sakamakon harin ƴan ta'addan Boko Haram a sansaninsu da ke jihar Borno na ci gaba da ƙaruwa.

Bayan kwana huɗu da kai harin na ƴan ta’addan Boko Haram a wani sansanin sojoji a ƙaramar hukumar Damboa, har yanzu ana neman dimbin sojoji da ba a san inda suke ba.

'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojoji a Borno
'Yan Boko Haram sun yi ta'asa kan sojoji a Borno Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce mayaƙan waɗanda suka zo cikin babbar tawaga, sun kai harin ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a ranar Asabar a sansanin sojoji na FOB da ke yankin Sabon Gari.

Kara karanta wannan

Yan bindigar da suka halaka sojoji sun gamu da ajalinsu, an harbe su har lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumomin sojoji a Maiduguri da birnin Abuja da gwamnatin jihar Borno ba su fitar da wata sanarwa dangane da lamarin ba.

Ƴan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojoji

Sai dai majiyoyi daga cikin rundunar sojoji sun bayyana cewa adadin waɗanda suka rasa rayukansu yana ci gaba da ƙaruwa.

Majiyoyin sun ce tawagar bincike ta sojoji na ci gaba da gano ƙarin gawarwakin jami'an tsaron da suka rasa ransu.

“An gano ƙarin gawarwaki, wasu sun mutu a hanyarsu ta zuwa asibiti a Maiduguri, yayin da sojoji da ƴan sa-kai masu yawa har yanzu ba a san inda suke ba, ana ci gaba da neman su."
"Ya yi wuri a bayyana yawan mutanen da muka rasa saboda har yanzu ana ƙirgawa. Ba zan iya bayyana adadin sojoji ko ƴan sa-kai da aka kashe ko sunayen jami’an da suka mutu ba, amma mun gano gawarwaki fiye da 12."

- Wata majiya

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Borno, 'yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya

Ƴan Boko Haram sun kwashe makamai

Wata majiyar sojoji mai sahihanci ta ce harin ya faru ne a sansanin FOB na rundunar 25TF Brigade da ke Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa.

Sansanin sojojin yana da alhakin kare kudancin Damboa, musamman hana ayyukan Boko Haram/ISWAP daga yankin jihar Yobe zuwa Chibok da Gwoza.

“An kore su gaba ɗaya daga sansanin, an kwashe wasu daga cikin kayan aikinsu yayin da aka lalata wasu."
"An turo ƙarin jami'ai daga babban sansanin 25TF Brigade tare da jami'an CJTF daga Damboa, amma bama-baman da ƴan ta'adda suka dasa sun tare su a kan hanya."
“Sakamakon haka, an raunata wasu daga cikin jami'an CJTF yayin da wasu suka mutu a kwanton-bauna. Kafin su isa Sabon Gari, mayaƙan Boko Haram sun bar wurin, bayan sun kwashe kayan aiki."
"Har yanzu ana tabbatar da bayanai, amma akwai sojoji da dama da ba a gano inda suke ba yayin da wasu suka rasa rayukansu."

Kara karanta wannan

Barazanar tashin bam: Gwamnatin Neja ta aika da muhimmin gargadi ga manoma

"Sansanin na FOB yana da ƙarfin sojoji 110, amma har yanzu kusan rabin wannan adadin kawai aka gano."

- Wata majiya

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP a jihar Borno.

Sojojin waɗanda suka saki bama-bamai a sansanin tantiran ƴan ta'addan sun hallaka da dama daga cikinsu tare da lalata kayan aikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng