Wani Gwamnan PDP Zai Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC? Gwamnati Ta Fito da Bayani

Wani Gwamnan PDP Zai Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC? Gwamnati Ta Fito da Bayani

  • Gwamna Sheriff Oborevwori ya musanta jita-jitar barin PDP, yana mai cewa makiyansa ne ke yada wannan labari marar tushe
  • APC ta zargi gwamnan da gazawa wajen samar da ababen more rayuwa duk da yawan kudin da jihar ke samu daga tarayya
  • Sai dai Gwamnan na Delta ya ce zarge-zargen 'yan adawa ba zai yi tasiri ba kuma zai ci gaba da kyautatawa jama'ar jiharsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Delta - Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya musanta jita-jitar cewa zai bar PDP ya koma jam'iyyar APC mai rike da mulki.

Jita-jitar ta nuna cewa gwamnan ya aika da wakilai zuwa wajen shugaban kasa Bola Tinubu don neman damar shiga jam’iyyar APC.

Gwamnan Delta ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa na shirin komawa APC
Gwamnan Delta ya ce yana cikin jam'iyyar PDP daram, ba zai sauya sheka zuwa APC ba. Hoto: @RtHonSheriff
Asali: Twitter

An yi ikirarin cewa gwamnan yana shakkar ko APC ta jihar za ta karbe shi cikin jam’iyyar ta su, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna ya canza sunan jami'a, ya raɗa mata 'Jami'ar Kashim Ibrahim'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Delta ya karyata jita-jitar komawa APC

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sir Festus Ahon ya fitar a ranar Litinin, ya ce wannan jita-jitar ba ta da tushe.

Sir Festus ya ce:

“Gwamna Oborevwori ya samu karbuwa daga al'ummar Delta da ke da kishin kasa, don haka babu dalilin da zai sa ya bar jam'iyyar PDP.”

Gwamnan ya roki jama’a da su yi watsi da jita-jitar sauya shekar, yana mai cewa ta fitowa ne daga makiyansa da ke neman kawo rudani.

Wannan musantawa ta biyo bayan sukar APC kan yadda gwamnatin Oborevwori ke tafiyar da lamura cikin jinkiri, duk da kudin da ake samu.

Gwamna ya zargi 'yan adawa da kulle-kulle

APC ta zargi gwamnan da rashin gudanar da ingantaccen aiki, inda ta yi ikirarin lalacewar ababen more rayuwa da rashin ci gaba a jihar.

Sai dai jaridar Punch ta rahoto Soir Festus yana martani da cewa:

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi magana kan gwamnan da ake tsoron zai sauya sheka zuwa APC

“Wasu a jam’iyyar adawa sun damu da karbuwa da hadin kan da gwamnan ke samu daga dukkanin bangarori na siyasar jihar.
“Don haka, gwamnan zai ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin tarayya don amfanin al'ummar jihar Delta da kasa baki daya.”

Gwamnan ya nanata cewa yana maida hankali kan cika alkawuran da ya daukarwa al'ummar Delta a lokacin yakin neman zabensa.

APC ta ce gwamnan jihar Delta ya gaza

APC ta bakin kakakinta, Valentine Onojeghuo, a Asaba, ta ce gwamnatin Oborevwori ta gaza cika alkawuran kawo ci gaba a jihar da ta dauka.

Jam'iyyar ce:

“Yawaitar lalacewar ababen more rayuwa da hanyoyin karkara sun jefa jama’a cikin wahalar zirga zirga da gudanar da harkokin kasuwanci.”
“Tashin hankalin da jama'a ke fuskanta da karancin ci gaba a karkashin mulkin Oborevwori sun mayar da tunanin samun ci ga a jihar ya koma mafarki."

'Yar majalisar Delta ta koma APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yar majalisar wakilai ta Ethiope, Hon. Erhiatake Ibori-Suenu, ta ce jam’iyyar PDP ta mutu a mazaɓarta da ke a jihar Delta.

Kara karanta wannan

LND: Ana shirin kafa sabuwar jam'iyya domin buga APC da kasa a 2027

Hon. Ibori-Suenu, ɗiyar tsohon gwamna James Ibori, ta bayyana cewa zuciyarta dama tun farko na tare da APC a siyasance, yanzu lokacin sauya sheka ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.