Tsohon Jami'in Gwamnatin El Rufai Ya Shiga Matsala, ICPC Ta Maka Shi Kotu

Tsohon Jami'in Gwamnatin El Rufai Ya Shiga Matsala, ICPC Ta Maka Shi Kotu

  • Hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ta fara ɗaukar matakin shari'a kan tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Nasir El-Rufai
  • ICPC ta kai ƙarar tsohon kwamishinan na kuɗi a lokacin gwamnatin El-Rufai ƙara a gaban kotu kan zargin almundahanar makudan kuɗi
  • An shigar da ƙarar ne a ranar Talata, 7 ga watan Janairun 2025 a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC, ta gurfanar da Alhaji Bashir Sa'idu, tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnati a lokacin Nasir El-Rufai, a gaban kotu.

Hukumar ICPC ta gurfanar da Alhaji Bashir Saidu, ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna, bisa zargin yin almundahana da kuɗi.

ICPC ta kai karar Bashir Sai'du
ICPC ta shigar da Bashir Sa'idi kara a gaban kotu Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

ICPC ta kai ƙarar jami'in gwamnatin El-Rufai

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an gurfanar da tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin ne a ranar Talata, 7 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi abin da za ta yi wa wadanda gobarar kasuwar Kara ta shafa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Bashir Saidu, wanda ya taɓa zama kwamishinan kuɗi a jihar Kaduna lokacin mulkin El-Rufai, an gurfanar da shi tare da wani Ibrahim Muktar, wanda ma’aikaci ne a ma’aikatar kuɗi.

A cewar ƙarar mai lamba FHC/KD/IC/2025, ana tuhumar waɗanda ake zargin da laifuka biyu na yin almundahana da kuɗi, rahoton da jaridar The Nation ya tabbatar.

Hakan ya saɓa da iƙirarin da aka yi a baya cewa an wanke Alhaji Bashir Saidu daga dukkan tuhume-tuhume bayan bincike na tsawon watanni 10.

Wane zargi ake yi wa kwamishinan El-Rufai?

Takardar ƙarar ta bayyana cewa a watan Maris na shekarar 2022, Alhaji Bashir Saidu, wanda a lokacin shi ne kwamishinan kuɗi, ya karɓi kudin haramun N155,000,000 daga hannun wani Ibrahim Muktar, wanda ya haura iyakar kudin da doka ta kayyade.

Kuɗin dai an karɓe su ta hannun Muazu Abdu, wanda shi ne mataimakinsa na musamman, inda hakan ya saɓawa sashe na 2(a) na dokar hana almundahanar kuɗi ta 2022, kuma hakan laifi ne da ya cancanci hukunci ƙarƙashin sashe na 19(d) na dokar.

Kara karanta wannan

Sokoto: Sakataren gwamnati ya shiga jarabawa, 'yarsa da jikoki 3 sun rasu lokaci daya

A cewar ICPC, a wannan lokacin a watan Maris 2022, Bashir Saidu, kai tsaye ko a fakaice ya karɓi kudin haramun na N155,000,000m daga hannun Muazu Abdu, wanda shi ne wakilinsa, daga hannun Ibrahim Muktar.

Ana zargin Bashir Saidu da karɓar kuɗin cin hanci

An tabbatar da cewa kudin suna da alaƙa da wata haramtacciyar harka, watau cin hanci, wanda hakan ya saɓawa sashe na 18(2)(d) na dokar hana almundahanar kuɗi ta 2022, kuma ya cancanci hukunci ƙarƙashin sashe na 18(3) na dokar.

Karar, wacce mataimakin babban jami’in shari’a na ICPC, Dokta Osuobeni Ekoi Akponimisingha, ya sanya wa hannu, an shigar da ita a ranar Talata, 7 ga watan Janairu, 2025, a babbar kotun tarayya da ke Kaduna.

El-Rufai ya ziyarci Bashir Sa'idu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya kai ziyara a gidan gyaran hali ga tsohon jami'in gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Tsohon sakataren gwamnatin jiha a Najeriya ya rasu

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ziyarci Alhaji Bashir Sa'idu, wanda aka tsare bayan hukumomi sun cafke shi bisa zargin almundahanar kuɗi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng