Hadimin Shugaban Ƙasa Ya Faɗi Jiha 1 da Kudirin Harajin Tinubu Zai Fi Yi Wa Illa

Hadimin Shugaban Ƙasa Ya Faɗi Jiha 1 da Kudirin Harajin Tinubu Zai Fi Yi Wa Illa

  • Taiwo Oyedele ya ce jihar Legas ce za ta fi asara idan Majalisar tarayya ta amince da sabon tsarin harajin da Bola Tinubu ya gabatar
  • Shugaban kwamitin sauya fasalin harajin ya yi bayanin yadda ake karɓar harahin VAT da yadda kamfanoni ke biyan harajin da ke kansu
  • Ya ce jihohi irinsu Legas da Ribas suna gaban kotu suna neman izinin tattara harajin da kansu saboda suna ganin ana tauye masu haƙki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kasafi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele, ya yi ƙarin haske kan sabon kudirin sauya fasalin haraji.

Mista Taiwo Oyedele ya bayyana cewa jihar Legas ce ta fi yin asara a shirin gyaran tsarin haraji na kasa wanda kudirorin ke gaban Majalisar Tarayya.

Taiwo Oyedele da Bola Tinubu.
Hadimin shugaban ƙasa ya yi bayani kan kudirin harahin Bola Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: Facebook

Ya ce shawarwarin kwamitin kan harajin kayayyaki wanda aka fi sani da VAT ya bayar, an tsara su ne domin amfanar dukkan shiyyoyin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Abuja: Bincike ya yi nisa, an gano wanda ya tashi bom a makarantar Islamiyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taiwo Oyedele ya faɗi haka ne yayin da yake martani kan ƙorafe-ƙorafen da suka biyo gabatar da kudirin harajin a cikin wani shiri na Arise TV.

Hadimin Tinubu ya faɗi jihar da za ta yi asara

Hadimin shugaban ƙasar ya ce yawancin kamfanoni da ke da cibiyoyinsu a jihar Legas suna biyan VAT dinsu a can saboda tsarin gudanarwar kuɗaɗensu.

A rahoton Daily Trust, Oyedele ya ce:

“Legas ce jihar da za ta fi asara a wannan doka saboda yawancin kamfanonin da ke da hedikwatarsu a jihar suna biyan VAT a can.
"Amma wannan gyaran dokokin harajin da aka ɓullo da shi zai ba kowane yanki damar amfana da kuɗaɗen da ake karɓa na haraji."

Harajin VAT: Wasu jihohi sun kai ƙara kotu

A bayanansa, Oyedele ya ce akwai wasu jihohi kamar Ribas da Legas da suka shiga kotu suna neman izinin karbar harajin VAT dinsu.

Kara karanta wannan

Gwamnan da ke sukar kudirin gyaran haraji ya koma goyon bayan tsarin Tinubu

A cewarsa, jihohin sun kai ƙara domin neman izinin ne saboda suna ganin ba su samun kaso mai tsoka duk da gudunmawar da suke bayarwa wajen tattara harajin.

Sai dai Oyedele ya yi gargadin cewa barin jihohi su karbi VAT din kansu zai jefa kasuwanci cikin rudani.

Yadda kamfanoni ke biyan haraji a Legas

A cewarsa:

“Idan jihohi suka fara karbar VAT a Najeriya, zai haifar da rudani ga kasuwanci saboda jihohi ba za su mutunta tsarin shiga da fitar haraji ba.”
"Idan kamfanoni suka tashi biyan VAT, suna bayarwa ne a hedkwatarsu, hakan ya sa MTN, BUA, Dangote, Airtel da galibin bankuna suna biyan harajinsu a Legas. Wasu daga cikin kamfanonin mai kuma a jihar Ribas.”

Sabon tsarin, a cewarsa, zai gyara rabon kudaden VAT wanda rage fifikon jihar Legas duk da babbar gudunmawar da take bayarwa.

Shugaba Bola Tinubu a watan Oktoban 2024 ya gabatar da kudirorin dokoki hudu na gyaran haraji ga Majalisar dokoki ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi abin da za ta yi wa wadanda gobarar kasuwar Kara ta shafa

Kwamitin haraji na fuskantar tangarɗa

A wani labarin, kun ji cewa kwamitin gyaran haraji na shugaban ƙasa ya bayyana cikas ɗin da ya samu a kokarin neman shawari daga masu zuwa da tsaki.

Taiwo Oyedele ya ce gwamnan Legas ne kaɗai ya amsa gayyatar kwamitin amma sauran gwamnonin kuma har yanzu zama da su bai yiwu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262