'Yan Bindiga Sun Bi Dare Sun Yi Garkuwa da Mutane Masu Yawa a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Bi Dare Sun Yi Garkuwa da Mutane Masu Yawa a Zamfara

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'asa a jihar Zamfara bayan sun kai mummunan hari a garin Gana
  • Ƴan bindigan sun yi garkuwa da mutane aƙalla 46 a garin da suka kai ranar Lahadi, 5 ga watan Janairun 2025
  • Mazauna garin sun bayyana cewa ƴan bindigan sun kuma ƙona gidaje masu yawa bayan sun banka musu wuta a yayin harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutane 46 a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ƴan bindigan sun sace mutanen ne da suka haɗa da mata da yara a garin Gana da ke jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara
'Yan bindiga sun sace mutane 46 a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A cewar rahoton Reuters, mazauna yankin sun ce harin ya auku ne da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun taso mutanen Zamfara a gaba, sun saka haraji mai tsoka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigan masu yawa da ke a kan babura sun kai hari a garin, yayin da suka riƙa harbe-harbe da ƙona gidaje da wuraren kasuwanci da dama.

Harin na zuwa ne kimanin wata ɗaya bayan da wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da aƙalla mutane 43 a Kakidawa da ke gundumar Gidan Goga a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Yadda ƴan bindiga suka yi ta'asa

Shaidun gani da ido sun ce ƴan bindigan sun yi ta harbe-harbe, lamarin da ya sa mazauna yankin suka tsere zuwa cikin daji.

Sun ce daga bisani ƴan bindigar sun riƙa shiga gida-gida, inda suka yi awon gaba da mata da ƙananan ycara da suka kasa tserewa.

Alhaji Garba Haure, wani basaraken gargajiya a Gana, ya ce ɗaukin da jami’an tsaron gwamnati suka kawo ne, ya hana maharan ƙona garin baki ɗaya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga, sun kubutar da mutane a Katsina

A cewarsa ba a samu asarar rayuka ba a yayin harin da ƴan bindigan suka kai a cikin dare.

"Muna da jimillar maza da mata da yara 46 da aka yi garkuwa da su, kuma har yanzu ana ci gaba da ƙirgawa."

- Alhaji Garba Haure.

Wani mazaunin garin mai suna Bala Harauma ya bayyana cewa adadin mutanen da aka sace na iya karuwa.

Wasu sun kuɓuta daga hannun ƴan bindiga

Bala Harauma ya ƙara da cewa mutane shida sun samu nasarar tserewa yayin da ƴan bindigan da suka sace su suke tafiya da su a safiyar ranar Litinin.

Wani mazaunin garin mai suna Yusuf Mohammed ya bayyana cewa ƴan bindigan sun ƙona gidaje da dama da rumbunan da ke ɗauke da kayan abinci.

Mutanen da aka yi garkuwa da su a harin na Disamba an sako su ne bayan an biya kuɗin fansa, kamar yadda mazauna garin suka bayyana.

Kara karanta wannan

Fadan Fulani da makiyaya ya barke a Jigawa, an samu asarar rayuka

Ƴan bindiga sun sanya haraji a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun ƙaƙaba haraji kan mutanen ƙauyuka 25 da ke yankin Tsafe ta Yamma a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun sa harajin N172m ga ƙauyukan guda 25, suka bayyana abin da kowannensu zai biya domin tsira daga sharrinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng