Miyagun Ƴan Bindiga Sun Kafa Sansani kusa da Inda Gwamna Ya Shirya Biki

Miyagun Ƴan Bindiga Sun Kafa Sansani kusa da Inda Gwamna Ya Shirya Biki

  • Gwamna Seyi Makinde ya yi ikirarin cewa 'yan bindiga na barazanar mamaye jihar Oyo, yayin da sojoji ke korarsu daga Arewa
  • Ya ce miyagun suna tserewa daga Arewa maso Yamma sakamakon luguden wuta da sojoji ke yi, amma yake cewa jihar za ta dakile su
  • Makinde ya bukaci sarakuna da al’umma da su rika bayar da rahoton duk wani motsi da ba su gamsu da shi ba domin daukar mataki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Gwamna Seyi Makinde ya yi Allah wadai da yadda wasu gungun 'yan ta'adda ke kai wa jihar Oyo mamaya a 'yan kwanakin nan.

Gwamnan ya lashi takobin kare jiharsa daga duk wata barazanar 'yan ta'adda da kuma wanzar da zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Gwamna Seyi Makinde ya tuna lokacin da 'yan bindiga suka yi sansani a kusa da inda ya yi taro
Gwamnan Oyo ya yi ikirarin cewa 'yan bindiga daga Arewa na barazanar mamaye jiharsa. Hoto: @seyiamakinde
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun yi sansani a kusa da gwamna

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun dauko salon fadada ta'addanci zuwa Kudancin Najeriya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Gwamna Seyi Makinde ya tuno da yadda wasu 'yan ta'adda suka yi sansani a kusa da inda ya yi bikin murnar karin shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wajen taron addinai na shekarar 2025 da aka gudanar a Agodi da ke Ibadan, Gwamna Makinde ya ce tazarar wurin taron da 'yan bindigar kilo mita biyu ne.

Makinde ya ce sun samu bayanan sirri cewa 'yan bindiga suna ta baro Arewa maso Yamma, zuwa jihar Oyo saboda tsoron hare-haren sojojin Najeriya.

"Yan ta'adda na shirin mamaye Oyo" - Makinde

A yayin taron, gwamnan na Oyo ya ce:

“Shekarar 2024 ta kasance mai cike da kalubale, musamman kan tsaro. Mun fuskanci gobara, fashi da makami, da garkuwa da mutane."

Ya kara da cewa:

“Amma a shekarar 2025, za mu ninka kokarinmu wajen magance wadannan matsaloli domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummarmu.”
"A taron tsaro na safiyar yau, na samu labarin cewa wasu miyagun mutane daga Arewa maso Yamma na shirin mamaye wannan jiha."

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun saki bama bamai a Neja, an halaka 'yan ta'adda da dama

Gwamna ya nemi hadin kan sarakunan gargajiya

Game da sansanin 'yan bindiga a kusa da inda ya yi taron murnar zagayowar shekara, Makinde ya ce:

"Lokacin da na ke bikin zagayowar ranar haihuwata, mun samu bayanan sirri cewa wasu 'yan bindiga sun kafa sansani kasa da kilomita biyu daga inda nake zama.”

Makinde ya gargadi al’umma da masu sarautar gargajiya da su rika bayar da rahoton duk wani motsin ba su yarda da shi ba ga jami'an tsaro.

“Masu sarautar gargajiya da al’umma, ku ba da hadin kai wajen sanar wa hukumomin tsaro bayanai na sirri idan kuka ga wani abu da ba ku yarda da shi ba.”

- Gwamna Seyi Makinde.

Gwamna zai tsaurara tsaro a jihar Oyo

Gwamnan jihar ya tabbatar da cewa zai yi duk mai yiwuwa don ganin cewa 'yan ta'adda ba su samu wurin zama ba a jihar Oyo, yana mai cewa:

"Ba zan huta ba sai tsaro ya tabbata a ko ina."

Kara karanta wannan

Ta ku ta kare: Sojoji sun shirya tsaf za su ga karshen 'yan ta'addan Najeriya a 2025

Makinde ya tabbatar da cewa za a ci gaba da daukar matakai masu tsauri don ganin jihar ta kasance cikin kwanciyar hankali.

'Yan bindiga sun sace jigon PDP a Oyo

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace jigon PDP a Oyo, Cif Benedict Akika, har cikin gidansa.

Miyagun sun harba bindiga lokacin da suka shiga unguwar Akika a Lagelu, sannan suka gargadi mutanen gidan da ka da su yi magana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.