Abuja: Bincike Ya Yi Nisa, An Gano Wanda Ya Tashi Bom a Makarantar Islamiyya
- Wasu baƙi ƴan jihar Katsina ne suka tashi bom a makarantar Islamiyya da ke garin Kuchibuyi a ƙaramar hukumar Bwari, Abuja
- Wani ganau ne ya tabbatar da hakan, ya ce bom ɗin ya tarwatse a lokacin da ɗaya daga cikinsu ke nunawa abokinsa abin da ya ɗauko
- Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa tuni ta cafke shugaban makarantar domin ya amsa tambayoyi kan lamarin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Wani shaidan gani da ido ya ba da labarin yadda bom ya tarwatse a wata makarantar Islamiyya ta almajirai da ke birnin tarayya Abuja ranar Litinin.
Wani ganau ya bayyana cewa ɗaya daga cikin ɗaliban makarantar Islamiyya ta Sani Uthman da ke kauyen Kuchibuyi a karamar hukumar Bwari ne ya zo da bom din a jaka.
Channels tv ts tattaro cewa tashin bom din dai ya hallaka almajirai biyu tare da jikkata wasu mutum biyu waɗanda ke kwance ana masu magani a asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa makarantar na da azuzuwa guda uku kuma an gina ta ne domin karatun almajirai watau makarantar tsangaya.
An gano wanda ya tashi bom a Abuja
Binciken da aka yi ya nuna cewa ɗalibin da ya je da bom makarantar ya zo ne daga jihar Katsina, kwana ɗaya kafin ranar da mummunan lamarin ya faru.
Wani ganau ya ce bom din ya tashi ne a lokacin da yaron ɗan Katsina ke nunawa ɗan uwansa da suka zo tare abin da ke kunshe a jakar.
Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
"Bam din ya tashi ne a daidai lokacin da yaron dan Katsina ya ke nuna wa wani yaro da ke makarantar abin. Wanda ke rike da bam din ya mutu nan take, yayin da ɗayan kuma ya rasu a asibiti."
Haka nan kuma mutum biyu sun jikkata, wata ƙaramar yarinya da ke karɓar magani a babban asibitin Kubwa da wani yaro da aka kwantar a asibitin koyarwa na jami'ar Abuja.
Tun bayan faruwar lamarin jami'an tsaro ciki har da dakarun ƴan sanda suka karɓe iko da makarantar.
Ƴan sanda sun kama shugaban makarantar
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta fitar ta ce an tura tawaga ciki har da ‘yan sandan sashin kwance bom zuwa wurin.
"Nan take bayan faruwar lamarin jami'an tsaro suka killace makarantar domin kare mazauna yankin da kuma gudanar da cikakken bincike.
"Rahoton binciken farko ya nuna cewa wasu mutane uku daga Katsina sun ziyarci mai makarantar Islamiyyar, Malam Adamu Ashimu. Baƙin ake zargin sun zo da bama-bamai.
"Biyu daga cikin baƙin ɗaliban da suka zo daga Katsina ne suka mutu sakamakon tashin bom ɗin, yayin da na ukun da wata yarinya da ke talla suka samu raunuka."
- Josephine Adeh.
Kakakin ƴan sandan ta ce yanzu haka sun cafke mai makarantar domin ya amsa tambayoyi kuma za a sanar da duk abin da aka gano, rahoton Vanguard.
Bom ya halaka almajirai 2 a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa bom din da ya tashi a makarantar Tsangaya a Abuja ya yi ajalin mutane biyu a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025.
An ruwaito cewa jami'an tsaro sun kai ɗauki wurin domin kwantar da hankulan mazauna garin da kuma dakile duk wata barazana da ka iya biyo baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng