'Yan Bindiga Sun Yi Ta'addanci ga Boka, Sun Kashe Masa 'Ya 'ya 3
- 'Yan bindiga sun kashe ‘ya’yan wani boka uku masu shekaru tsakanin biyu zuwa shida a garin Nise da ke a wani yanki na Jihar Anambra
- Maharan sun kutsa kai cikin gidan bokan, suka kashe yaran, sannan suka jefa gawarwakinsu a cikin wata mota da ke cikin gidan
- Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta fara bincike kan musabbabin harin da 'yan bindigar suka kai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano -‘Yan bindiga sun kashe ‘ya’ya uku na wani boka, a garin Nise da ke Karamar Hukumar Awka ta Kudu a Jihar Anambra.
Lamarin ya faru ne a daren Asabar, inda maharan suka shiga gidan bokan, suka kashe yaran sannan suka jefa gawarwakinsu a cikin wata mota da ke a harabar gidan.

Kara karanta wannan
Bikin cika shekara: Yadda uwa ta shafe kwanaki tana kirga kudin da baki suka watsawa 'yarta

Source: Original
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ‘yan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin, tare da bayyana cewa suna gudanar da bincike a halin yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kashe 'ya'yan boka 3
Rahotanni sun bayyana cewa mahara sun tsallaka katangar gidan wani boka, suka kutsa kai cikin dakin da yaransa ke ciki suka kashe su.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa maharan sun jefa gawarwakin yaran uku a bayan wata mota kirar Mercedes Benz da ke a harabar gidan.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da cewa an kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ‘yan sanda da ke yankin a ranar Lahadi.
A cewarsa, SP Tochukwu Ikenga;
“Mun samu rahoton kisan yaran uku daga DPO na yankin. An sanar da mu cewa maharan sun shiga gidan bokan suka kashe yaran, sannan suka jefa gawarwakinsu a cikin mota.”
Gudunmawar rundunar ‘yan sanda
Tochukwu Ikenga ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru kuma sun dauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro a yankin.
“Mun je wurin da lamarin ya faru, mun tattauna da wadanda ke kusa da wajen da mahaifin yaran don samun bayanan da za su taimaka mana wajen gano wadanda suka yi aika-aikar.”
- SP Tochukwu Ikenga
Har ila yau, rundunar ‘yan sanda na bincike domin gano musabbabin kisan, tare da yiwuwar binciken halin da mahaifin yaran ke ciki ko akwai kuskuren sa wajen kare lafiyar ‘ya’yansa.
Abin da mazauna yankin suka fada
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa mahaifin yaran na kulle su a cikin daki idan zai fita aiki tare da mahaifiyarsu, wanda ya sa aka fara zargin rashin kula da lafiyar yaran.
Rundunar ‘yan sanda ta yi kira ga jama’a da su bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen gano wadanda suka aikata mummunan aikin.
Sojoji sun firgita Bello Turji a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kai zafafan hare hare kan 'yan ta'adda masu alaka da fitaccen dan bindiga Bello Turji.
Harin da sojojin suka kai ya jawo kashe manyan 'yan ta'adda da ke tare da Bello Turji yayin da hakan ya sanya shi firgita ya fara buya a cikin daji kamar bera.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

