Gwamnan da ke Sukar Kudirin Gyaran Haraji Ya Koma Goyon Bayan Tsarin Tinubu
- Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana karin goyon baya a kan kudirin gyaran harajin Bola Ahmed Tinubu
- Gwamnan ya ce yanzu an fayyace yadda rabon kudaden VAT zai gudana tsakanin wuraren samar da kayayyaki da masu amfani da su
- Gwamnan ya koka kan yadda muhawarar kudirin gyaran haraji ta samu shiga daga mutane da ba su fahimci yadda tsarin VAT yake ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Nasarawa - Gwamnan Nasarawa, Malam Abdullahi Sule, a ranar Litinin ya bayyana cewa babu bukatar a janye kudirin harajin gwamnatin tarayya.
Gwamnan ya ce karin tabbacin da shugaba Bola Tinubu da Shugaban Kwamitin Shawara kan Manufofin Kudi da Gyaran Haraji ya yi zai wadatar.
A labarin da Arise News ta wallafa, ya ce irin wadannan bayanai sun taimaka wajen karin haske a kan bayanan da ya shigewa jama’a duhu a kan kudirin harajin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Sule ya kara da cewa ganawa tsakanin kwamitin haraji ta Taiwo Oyedele da gwamnonin jihohi da sarakunan gargajiya sun warware matsaloli da dama.
Gwamna ya damu kan kudirin haraji
This day ta wallafa cewa gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna damuwa cewa muhawarar kan kudirin gyaran haraji ta fada hannun mutane daban-daban.
Ya ce alamu sun nuna wadannan mutane ba su da masaniya kuma ba su da ba su fahimci abubuwan da kudirin harajin Bola Tinubu ya kunsa ba.
Gwamnan ya kara da cewa sun samu karin bayani a kan bangarorin kudirin harajin da ya shige wa gwamnoni da sauran jama’a, musamman wadanda ke Arewa a cikin duhu.
An yi wa gwamnonin bayanin kudirin haraji
Gwamnan jihar Nasarawa ya bayyana cewa sun samu karin bayanai da suka sha banban da abin da aka rika fada a kan kudirin harajin gwamnatin tarayya.
Gwamnan ya ce:
“A yayin taron da aka yi a Kaduna, abin da aka fada mana a lokacin shi ne cewa VAT zai kasance kawai a wurin samar da kudaden, inda kashi 60% za a bayar.”
“Oyedele ya tabbatar cewa, a’a, zai bambanta. 60% da ake magana akai za a raba shi tsakanin wurin masu samar da kaya da masu amfani da shi.”
Ya kara da cewa kamata ya yi masu ruwa da tsaki su kwantar da hankulansu a domin ana warware kalubalen da aka samu a cikin kudirin harajin.
Haraji: Tinubu ya fara lallaba manyan Arewa
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tashi tawaga domin ta shawo kan manyan Arewa domin su amince da kudirin haraji da gwamnatinsa ta bijiro da shi.
Dattawan Arewa, gwamnoni da masu ruwa da tsaki sun bijerewa kudirin harajin, wanda shugaban kasa ya gabatar a matsayin sharadin karbar basussuka daga Bankin Duniya.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa za nemi shawo kan matsalolin da ake fuskanta, domin tabbatar da cewa ana sa ran za a cimma nasarar jawo hankalinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng