Gwamna Radda Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa, Ya Shawarci Sabon Kwamishina
- Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwa don inganta manufofin gwamnatinsa
- An nada Malik Anas wanda ya kasance tsohon Akanta-janar na jihar Katsina a matsayin sabon kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki,
- Gwamna Radda ya bukaci kwamishinonin da aka nada da sauya wa matsayi su dage wajen kawo cigaba da kyautata rayuwar al’ummar jihar
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa tare da yin wasu sauye-sauye na musamman
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya amince da sauye-sauye a majalisar zartarwarsa don inganta gwamnatinsa.
A sauye-sauyen, an nada Alhaji Malik Anas, sabon zababben kwamishina da zai jagoranci ma’aikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki.
Gwamna Yadda ya yi sauye-sauye a gwamnatinsa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafin X a daren jiya Litinin 6 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabon kwamishina, Alhaji Malik Anas ya yi digiri na biyu a fannin kasuwanci daga Jami’ar Bayero, Kano, tare da samun gogewa a harkokin kudi da tsare-tsare.
Malik ya taba rike matsayin Akanta-janar na jihar Katsina kuma mamba ne a kungiyoyin kwararru da suka hada da hukumar haraji ta Najeriya.
Sauran wadanda sauye-sauyen ya shafa a gwamnatin Katsina
Har ila yau, an sauya Alhaji Bello Husaini Kagara daga ma’aikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki zuwa ma’aikatar kudi.
Hon. Bashir Tanimu Gambo, wanda ya jagoranci ma’aikatar kudi, yanzu zai riƙe ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin sarakunan gargajiya.
Sai kuma Alhaji Yusuf Rabi’u Jirdede, wanda ya shugabanci ma’aikatar ayyuka na musamman, an tura shi zuwa ma’aikatar kasuwanci, ciniki da zuba jari.
Sannan an sauya Alhaji Adnan Nahabu daga ma’aikatar kasuwanci, ciniki da zuba jari zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman.
Dikko Radda ya ba kwamishinoni shawara kan mulki
Gwamna Radda ya yi kira ga duka kwamishinonin da aka nada da kuma sake musu matsayi da su jajirce wajen kyautata ayyukansu don ciyar da jihar gaba.
Ya umarci sabon kwamishina, Alhaji Malik Anas da ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa ta daidaita da manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa a jihar.
Gwamna Abba Kabir ya yi sababbin nade-nade
A baya, mun ba ku labarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada sababbin masu ba da shawara na musamman, ciki har da Hon. Ahmad Speaker da Injiniya Ahmad.
Rahotanni sun tabbatar cewa an gudanar da bikin rantsar da wadanda aka nada a ranar Litinin, 6 ga Janairu, a gidan gwamnatin Kano da misalin karfe 11:00 na safe.
Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir ne ya sanar da hakan a ranar Lahadi, 5 ga watan Janairun 2025 inda taya wadanda aka ba muƙaman murna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng