Rahoton Ofishin Babban Oditan Kasa Ya Zargi NNPCL da Zambar N514bn
- Ofishin Odita Janar na Najeriya ya zargi Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) da karkatar da wasu kudade
- Ana zargin NNPCL da ware kudaden da sunan gudanar da ayyukan farfado da matatun da ya mallaka a jihohin Najeriya
- NNPCL dai ya bayyana yadda ya kashe akalla $2bn wajen gyaran matatun Fatakwal da Warri, kuma ana sa ran gyara ta Kaduna
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Ofishin Odita Janar na Najeriya ya zargi kamfanin mai na kasa (NNPCL) da zambar Naira biliyan 514 bayan an binciki asusun kamfanin. Wannan zargi na kunshe ne a cikin rahoton shekara-shekara na ofishin Babban Odita na masa ya fitar na shekarar 2021, wanda aka buga a watan Nuwamba 2024 kuma aka saki kwanan nan.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa rahoton ya bayyana cewa NNPCL ta karkatar da kudade da kuma yin amfani da wasu kudaden da aka ware domin Asusun Tarayya ba bisa ka’ida ba a shekarar 2021.
Ana zargin NNPCL da fitar da kudade
Jaridar ICIR ta wallafa cewa bayanan sun nuna cewa ana zargin NNPCL da yin cire-ciren kudi ba bisa ka'ida ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ga nuna cewa Kamfanin na NNPCL ya kuma cire Naira biliyan 82.9 daga kudaden Asusun Tarayya don gyaran matatun mai.
An soki tsarin cirar kudin NNPCL
Ofishin Odita Janar ya yi suka kan cire kudade daga kudaden da aka sayar da danyen mai na cikin gida kai tsaye daga tushe, ba tare da neman izini ba.
Rahoton ya gano cewa an cire Naira biliyan 82.9 ta daga sayar da danyen mai da iskar gas daga bayanan shekarar 2020 da 2021
Dalilin kamfanin NNPCL na cire kudade
Rahotannin sun bayyana cewa kamfanin NNPCL ya ce ya bayyana cewa an yi hakan don gyaran matatun mai a kasar nan.
Rahoton ya kara da cewa an bayyana cewa babu wasu takardun da ke nuna izini ko amincewar hukumomin da suka dace kafin cire kudaden
Ana zargin NNPCL da satar kudade
Rahoton ya ce wannan matakin da NNPCL ya dauka ya fi kama da karkatar da kudaden da ya kamata su shiga asusun tarayya Ya ce bayanai sun nuna NNPCL ya samu jimlar Naira biliyan 484.7 daga kudaden sayar da danyen mai na cikin gida a watan Maris da Mayu 2021. Rahoton ya kuma nuna cewa Naira biliyan 343.6 an “cire kai tsaye” daga kudaden sayar da danyen mai na cikin gida don cike ginin aikin kamfanin.
NNPCL ya fara gyara matatar Kaduna
A baya, kun ji cewa kamfanin mai na kasa (NNPCL), ya bayyana fara gyara matatar mai ta Kaduna, bayan gyara matatun Fatakwal da na Warri a shekarar 2024
Kamfanin NNPCL ya ce an samu nasarar farfado da matatun biyu domin fara aiki bayan kashe akalla $2bn, inda ake sa ran za a gyara dukkanin karatun mai mallakin kasa guda hudu.
Wannan ya na kunshe a cikin martanin da Kamfanin ya yi wa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo na zargin cewa an kashe kudi ne a banza, amma matatun ba sa aiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng