Babban Malamin Musulunci Ya Rasu a Najeriya, Farfesa Pantami Ya Magantu

Babban Malamin Musulunci Ya Rasu a Najeriya, Farfesa Pantami Ya Magantu

  • Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar fitaccen malamin Musulunci a jihar Gombe
  • Sheikh Isa Pantami ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, Sarkin Malaman Funakaye, Malam Adamu Abubakar Bajoga
  • Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi 5 ga watan Janairun 2025 wanda aka gudanar da jana'izarsa a safiyar Litinin 6 ga watan Janairun 2025

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Bajoga, Gombe - An shiga alhini bayan sanar da rasuwar fitaccen malamin Musulunci a jihar Gombe, Malam Adamu Abubakar Bajoga.

Marigayin ya rasa ransa ne a ranar Lahadi 5 ga watan Janairun 2025 inda aka yi jana'izarsa a safiyar ranar Litinin a garin Bajoga da ke jihar Gombe.

Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar malamin Musulunci a Gombe
Farfesa Pantami ya tura sakon ta'aziyya bayan rasuwar babban malamin Musulunci a Gombe. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Asali: Facebook

An yi jana'izar babban malamin Musulunci a Gombe

Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya mika sakon ta'aziyyarsa a gajeren rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Rarara ya tabo tsuliyar dodo, an ba shi wa'adi ya janye kalamansa kan shugaban Nijar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni da mu ke samu sun tabbatar da cewa an yi jana'izar marigayin a garin Bajoga, hedikwatar karamar hukumar Funakaye a jiya Litinin.

Jana'izar ta samu halartar manyan mutane ciki har da tawagar Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya karkashin jagorancin shugaban ma'akatan fadar gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Inuwa Kari.

Har ila yau, shugaban karamar hukumar Funakaye, Hon. Abdul Rahman Shuaibu da takwaransa na Nafada, Babangida Adamu Jigawa sun samu halartar sallar jana'izar.

Farfesa Pantami ya yi ta'ziyya ga iyalan marigayin

Farfesa Pantami ya ce tabbas an yi babban rashin malami kuma mutumin kirki wanda ya ba da gudunmawa sosai ga al'umma.

"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un!."
"Muna mika ta'aziyyar rasuwar babanmu, Sarkin Malaman Funakaye, Malam Adamu Abubakar Bajoga wanda ya rasu a jiya Lahadi."
"Muna kara mika ta'aziyyar zuwa ga iyalansa, musamman CSP Sani Adamu Bajoga da sauran zurriyyar marigayi tare da addu'ar Allah ya ba da hakuri ga yan'uwa da iyalai kan wannan babban rashi."

Kara karanta wannan

Rarara ya tara malamai 1,000 domin neman tsari daga sharrin bokayen Nijar, an yi addu'oi

- Farfesa Isa Ali Pantami

Gudunmawar da malamin ya ba addinin Musulunci

Pantami ya ce marigayin ya bar babban tarihi a rayuwarsa, wanda zai ci gaba da zama abin alfahari ga zuriyarsa da al'umma baki daya.

A karshe, Pantami ya yi addu'ar Allah ya sa wannan rashi ya zama rahama gare shi, kuma ya hada shi da iyaye da malamai da suka rasu a cikin aljanna Firdausi.

Al'umma da dama sun nuna alhin kan rasuwar malamin da suka ce ya ba da gudunmawa musamman ga addinin Musulunci.

Gogaggen malamin Musulunci ya rasu a Gombe

A baya, kun ji cewa a safiyar ranar Laraba 13 ga watan Nuwambar 2024 aka sanar da rasuwar shahararren malamin addinin Musulunci, Gwani Muhammad Sani a jihar Gombe.

An ruwaito cewa Sheikh Gwani Muhammad Sani ya shafe shekaru yana karantar da ɗalibai Alkur'ani daga dukkan sassan Arewacin Najeriya.

Wani daga cikin dalibansa a jihar Gombe ya tabbatar da cewa an yi masa sallah a safiyar ranar da misalin karfe 11:00 a kofar gidansa da ke garin Gombe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.