Gwamna Ya Fusata da Kashe Bayin Allah, Ya Sanya Dokar Zaman Gida a Jiharsa
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya sanya dokar hana fita daga safiya zuwa yammacin kowace rana a Owo, hedkwatar karamar hukumar Owo a Ondo
- Hakan dai ya biyo bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin wasu ƴan kungiyoyin asiri masu adawa da juna wanda ya yi sanadin kashe jigon APC
- An ruwaito cewa rikicin ya fara ne ranar Lahadi, inda ya ci gaba da faruwa a garin na Owo har zuwa washe garin yau Litinin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Gwamnan Ondo, Hon. Lucky Aiyedatiwa, ya ayyana dokar hana fita daga asuba zuwa yamma a garin Owo, hedikwatar karamar hukumar Owo da ke jihar.
Gwamna Aiyedatiwa ya ɗauki matakin ƙaƙaba dokar kulle a garin ne bayan rikicin kungiyoyin asiri da ya ɓarke a garin.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa rikici ya barke a Owo ranar Litinin sakamakon musayar wuta da ake zargin 'yan kungiyar asiri biyu masu adawa da juna sun yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin Owo ya fusata Gwamna Aiyedatiwa
Lamarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutane hudu ciki har da wani babban jigon APC kuma tsohon shugaban matasa a Owo.
Baya ga ɗan siyasar, an kuma kashe wasu mutane uku da suka hada da wata uwa da danta da suka zo wucewa ba tare da sanin abin da ake faruwa ba.
Bayanai sun nuna an kashe masu wucewar ne a lokacin da miyagun suka kai harin ramuwar gayya kan abokan faɗansu bayan harin farko.
Bisa ga rahotanni da suka fito, faɗan ƴan ƙungiyoyin asirin ya fara ne a ranar Lahadin da ta gabata kuma suka ci gaba har zuwa safiyar Litinin.
Gwamnan Ondo ya sa sokar zaman gida a Owo
Sai dai a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Ebenezer Adeniyan, ya fitar, Gwamna Aiyedatiwa ya umarci duk mazauna garin su zauna a gida.
Gwamnan ya sanar da sanya dokar zaman gida tun daga kowace safiya har dare domin tabbatar da bin doka da oda a garin Owo.
Hon. Aiyedatiwa ya ce:
"Sakamakon rikicin kungiyoyin asiri da ya faru a Owo, wanda ya jawo asarar rayuka da rashin tsaro, gwamnan Ondo, Hon. Lucky Aiyedatiwa, ya ayyana dokar hana fita daga asuba zuwa yamma a garin har sai baba ta gani.
“Ya zama wajibi dukkan mazauna garin su ci gaba da zama a gida saboda biyayya ga dokar hana fita.
"Sai dai kawai ayyuka masu muhimmanci, kamar asibitoci, ayyukan gaggawa, da jami’an tsaro, ne za su samu rangwame daga wannan doka.”
Gwamna ya umarci hukumomin tsaro su dage
Gwamna Aiywdatiwa ya kuma umarci hukumomin tsaro su tabbatar da cewa jama'a sun yi biyayya ga dokar hana fitar da ya sanya domin kare lafiyarsu.
Har ila yau, ya umarci jami'an tsaro su binciko tare da kama wadanda suka haddasa tashin hankali, sannan su dawo da zaman lafiya, Punch ta rahoto.
Matar Akeredolu ta soki Gwamnan Ondo
A wani rahoton kun ji cewa matar marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo ta caccaki Gwamna Lucky Aiyedatiwa bisa yunkurin shirya taron tunawa da mijinta.
Betty Akeredolu taron da gwamnatin Ondo ta shirya damfara ce domin babu wanda ya gayyaci iyalan marigayi Akeredolu.
Asali: Legit.ng