EFCC: Wasu Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya Sun Shiga Matsala, An Kore Su daga Aiki
- Hukumar EFCC ta sallami ma'aikata 27 bisa samunsu da hannu a aikata laifukan rashawa da rashin ɗa'a a shekarar 2024
- Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya jaddada kudirin hukumar na hukunta duk wanda ya aikata rashin gaskiya a cikin jami'anta
- EFCC ta bayyana cewa tana da masaniyar wasu na ƙoƙarin ɓata sunan jami'anta kuma za ta ɗauki matakin da ya dace
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kori ma’aikata 27 daga aiki a shekarar 2024 kan aikata laifuffukan rashawa da rashin da’a.
Hukumar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa na jama'a, Dele Oyewale ya fitar a ranar Litinin.
EFCC ta kuma wallafa sanarwar a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter a yau Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta kori ma'aikata a shekarar 2024
Sanarwar ta jaddada cewa hukumar EFCC ba za ta lamunci cin hanci ba, kuma duk wani zargi da aka samu kan wani ma’aikacinta za ta yi bincike sosai.
Kakakin EFCC, Oyewale ya bayyana cewa:
“An sallami ma’aikatan ne saboda laifuffukan rashawa da rashin da’a kuma mun yi wannan hukuncin ne bayan shawarwarin kwamitin ladabtarwa na EFCC, wanda shugaban hukumar, Mr. Ola Olukoyede, ya amince da shi.
“Olukoyede ya jaddada kudirin EFCC na rashin sassauci kan cin hanci, yana gargadin cewa ba wani ma’aikaci da zai tsira daga ladabtarwa idan aka same shi da laifi.
“Haka kuma, EFCC na kara sanar da jama’a kan ayyukan masu yin kutse da yin zagon kasa suna amfani da sunan shugabanta don karbar na goro daga wadanda ake bincika."
EFCC ta shafa hodar ba sani da sabo
Dele Oyewale ya duk wani zargi komai kanƙantarsa game da wani ma'aikacin EFCC ba za a bar shi ya tafi sakaka ba, za a bincika a gano gaskiya.
Ya ce hukumar ta sha alwashin bincike kan zargin neman Dala 400,000 da wata ma'aikaciyar EFCC ta yi duk da ba a gano wacece ba a halin yanzu.
Shugaban EFCC mutum ne mai gaskiya
“Bugu da ƙari, an gurfanar da wasu da ake zargi, Ojobo Joshua da Aliyu Hashim, a gaban Mai Shari’a Jude Onwuebuzie na ɓabban kotun birnin tarayya Abuja.
"Ana zarginsu da neman cin hancin Dala miliyan daya daga tsohon Manajan Darakta na jukumar tashoshin ruwa ta Najeriya, Mohammed Bello-Kaka.
“Shugaban EFCC, Olukoyede mutum ne mai gaskiya kuma ba zai taba yarda wasu kuɗi su ruɗe shi ba. Jama’a na da hakkin sanar da hukumar kan masu irin wannan dabi’ar.
- Dele Oyewale.
Haka kuma, EFCC ta ce tana da masaniya kan wasu shirye-shirye da ake yi domin bata sunan jami’an hukumar ta hanyar wasu dabaru, inda ta ce ba za ta lamurci hakan ba.
Yadda EFCC ta kwato biliyoyin Naira
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta samu manyan nasarori a yaƙin da take da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa.
Fadar shugaban ƙasa ta ce EFCC ta kwato biliyoyin Naira daga hannun ɓarayi marasa gaskiya, sannan ta yi nasarori a shari'o'in da ta shigar da dama a gaban kotu.
Asali: Legit.ng