'Bello Turji Ya Firgita Yana Buya a Ramuka Kamar Beran Daji,' Sojoji

'Bello Turji Ya Firgita Yana Buya a Ramuka Kamar Beran Daji,' Sojoji

  • Sojojin rundunar Operation Fansar Yamma sun tabbatar da cewa Bello Turji yanzu yana rayuwa kamar beran daji yana buya a rami
  • Rundunar ta kai farmaki kan sansaninsa da ke Karamar Hukumar Shinkafi, inda jiragen yakin sojoji suka lalata sansaninsa
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda ciki har da kashe wani shahararren dan ta’adda, Sani Rusu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jjihar Zamfara- Kakakin rundunar Operation Fansar Yamma, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya ce Bello Turji ya dawo kamar beran daji yana buya a ramuka.

Laftanar Kanal Abdullahi ya ce rundunar ta lalata sansanonin Turji da ke Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara ta hanyar hadin gwiwar jiragen yaki da sojojin kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi abin da za ta yi wa wadanda gobarar kasuwar Kara ta shafa

Sojoji
Sojoji sun ci karfin Bello Turji. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa an kai farmakin ne bayan Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare kan al’ummar Shinkafi idan har ba a saki danginsa da aka kama ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An lalata sansanonin Bello Turji a Shinkafi

Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya bayyana cewa jiragen yakin rundunar Fansar Yamma sun kai farmaki cikin nasara kan sansanonin ‘yan ta’adda da ke Shinkafi.

“Jiragen yakinmu sun yi mummunan barna ga sansanonin ‘yan ta’adda a Karamar Hukumar Shinkafi.
An kashe mayaka da dama na Turji, yayin da shi kansa yanzu ke buya kamar beran daji a ramuka.”

- Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi

A cewarsa, nasarar ta kara wa rundunar kwarin gwiwar ci gaba da aikin kawar da sauran ‘yan ta’adda a yankin da kewaye.

Sojojin kasa da ke aiki tare da jiragen yaki sun tabbatar da cewa za su ci gaba da lalubo sauran sansanonin da suka rage.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar Bello Turji, sojoji sun kashe ɗan ta'addan da aka daɗe ana nema

Barazanar Turji ga al’ummar Shinkafi

Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare kan mutanen Shinkafi idan ba a saki wasu daga cikin danginsa da ake zargi da hannu da ta’addanci ba.

Bayan wannan barazana, rahotanni sun tabbatar da cewa Turji ya jagoranci wasu hare-hare da suka hada da sace fasinjoji a yankin, wanda ya saka sojoji kai farmaki.

Turji
Kasurgimin dan ta'adda, Bello Turji sanye da kayan jami'an tsaro
Asali: Twitter

A sakamakon farmakin, rundunar Fansar Yamma ta kashe mayakan Turji da dama, ciki har da wani babban jagoran ‘yan ta’adda, Sani Rusu, wanda shima ya dade yana addabar al’umma.

Za a ci gaba da yakin da ‘yan ta’adda

Rundunar Fansar Yamma ta sha alwashin ci gaba da yakar sauran ‘yan ta’adda da suka rage a yankin Arewa maso Yamma.

Laftanar Kanal Abdullahi ya tabbatar da cewa rundunar tana da kwarin gwiwar ganin karshen duk wani ta’addanci da ya dabaibaye yankunan Zamfara da kewaye.

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun saki bama bamai a Neja, an halaka 'yan ta'adda da dama

Harin da aka kai kan sansanonin ‘yan ta’adda a Shinkafi ya zama wani muhimmin ci gaba wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar yankin.

An yi kofar rago ga Bello Turji

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar tsaron Najeriya ta ce ta yi kofar rago ga kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji.

Babban Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce an gama kakkabe miyagun da ke tallafawa dan ta'addar saura cafke shi ne kawai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng