Abin Fashewa da Ake Zaton 'Bom' Ne Ya Tarwatse a Makarantar Islamiyya, Ɗaibai Sun Mutu
- Ɗalibai biyu sun mutu da wani abin fashewa ya tashi a makarantar Islamiyya da ke yankin ƙaramar hukumar Bwari a birnin tarayya Abuja
- Wata majiya ta ce ana zargin wani sabon ɗalibi ne ya zo da abin fashewar da ake zaton bom ne, ɗalibai da dama sun ji raunuka
- Duk da babu sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda, bayanai sun nuna jami'an tsaro sun kai ɗauki makarantar kuma sun fara bincike
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Wani abin fashewa da ake zaton bom ne ya tarwatse a wata makarantar Islamiyya da ke yankin babban birnin tarayya Abuja.
Mummunar fashewar dai ta yi sanadiyyar mutuwar dalibai biyu da jikkata wasu dalibai hudu kawo yanzu.
Wani jami'in tsaro ya shaidawa Premium Times cewa lamarin ya faru da misalin karfe 12 na tsakar ranar Litinin a wata makarantar Islamiyya da ke kauyen Kuchibiyu a yankin Bwari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa garin da wannan iftila'i ya faru na da nisan kilomita 42 Uwa tsakiyar birnin Abuja.
Jami'an tsaro sun kai ɗauki makarantar
Wata majiyar ta ce jami'an tsaro ciki har da dakarun ƴan sanda na sashen kwance bam sun isa wurin yayin da aka kai waɗanda suka jikkata asibiti.
Har yanzu dai babu wani cikakken bayani daga rundunar 'yan sandan Abuja kan ainihin abin da ya faru da alƙaluman waɗanda fashewar ta shafa.
Da aka tuntubi jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, Josephine Adeh, ta wayar tarho ba ta ɗaga kiran ba har kawo yanzu.
Abuja: Yadda bom ya tarwatse a Islamiyya
Sai dai wata majiya daga cikin jami'an tsaro da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:
"Dalibin da ya mutu, wanda ba a tabbatar da sunansa ba har yanzu, shi ke dauke da abin fashewar wanda ake zargin bom ne, yayin da ya tarwatse ya raunata wasu ɗalibai.
"Lamarin ya haifar da tashin hankali a makarantar da yankin gaba ɗaya, amma har yanzu ba mu ji karin bayani da mahukuntan makarantar ba tukunna."
Majiyar ta kara da cewa daliban da lamarin ya shafa sun kasance sababbi da aka yi musu rajista a makarantar kwanan nan kuma sun fara zuwa karatu ranar 3 ga watan Janairu.
Ƴan sanda suna zargin shugaban makarantar
Lamarin dai ya isa kunnen DPO na ƴan sandan yankin, wanda ya ɗauki jami'an sashen kwance bom suka kai ɗauki wurin.
A rahoton masaniyat farko, ƴan sandan sun tabbatar da cewa ɗalibai biyu sun mutu, wasu biyu kuma na kwance ana masu magani a asibiti.
A cikin rahoton rundunar ‘yan sandan ta ce wasi ɓaƙi daga Katsina sun ziyarci shugaban Islamiyyar, Adamu Ashimu kuma su suka zo da bama-baman.
Ƴan sanda sun kama.shugaɓan makarantar kuma sun ce za su masa tambayoyi kafin si fitar da sanarwa a hukumance.
Yan sandan Abuja 140 sun mutu a 2024
A wani labarin, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Abuja ta bayyana cewa jami'anta 140 sun rasa rayukansu daga farko zuwa karshen 2024.
Rundunar ta bayyana cewa wasu daga ciki sun rasu ne a bakin aiki yayin yaƙi da ta'addanci yayin da wasu kuma suka mutu sakamakon ciwo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng