Barazanar Tashin Bam: Gwamnatin Neja Ta Aika da Muhimmin Gargadi ga Manoma
- Gwamnatin jihar Neja ta gargaɗi mazauna wasun yankunan jihar kan ababen fashewa da aka binne a gonakinsu
- Gwamnatin ta buƙaci manoma su yi taka tsantsan da zuwa gonakinsu gabanin sojoji su kammala cire bama-baman da aka binne
- Gwamnan jihar ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci a jihar tare da haɗin kan jami'an sojin saman Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Minna, jihar Neja - Gwamnatin Jihar Neja ta gargadi mazauna wasu yankuna na jihar, inda ta buƙace su da su guji zuwa gonakinsu a halin da ake ciki domin kaucewa fadawa tarkon ababen fashewa da ‘yan bindiga suka dasa.
A watan Agustan 2024 ne dai ‘yan bindiga suka kashe aƙalla manoma 13 a ƙauyen Alawa da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar.
Jaridar The Punch ta ce ‘yan bindigar sun bi manoman har zuwa gonakinsu, inda suka kashe su saboda zargin cewa sun ba da bayanan sirri game da motsinsu ga jami’an tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ba manoman jihar Neja shawara
Kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar ta Neja, Bello Abdullahi ne ya yi wannan gargaɗi a Minna babban birnin jihar, yayin wani biki na shekarar 2024 da aka gudanar a sansanin rundunar 013 na sojin saman Najeriya da ke Minna.
Kwamishinan ya bayyana cewa akwai buƙatar a jira sojoji su cire bama-bamai da sauran ababen fashewa a wuraren da ake zargin an dasa su, kafin mazauna yankin su samu damar yin zirga-zirga cikin kwanciyar hankali.
“Muna gargaɗin manoma da su yi taka-tsan-tsan wajen zuwa gonaki a halin yanzu. ‘Yan bindiga sun turbuɗe ababen fashewa a cikin ƙasa domin barazana ga rayuwar jama'a."
"Dole ne a jira sojoji su fara bincike yankunan da ake zargin an dasa bama-baman kafin a iya samun damar shiga wuraren,”
- Bello Abdullahi.
Gwamnan ya yaba da ƙoƙarin da sojoji
Kwamishinan wanda ya wakilci Gwamna Mohammed Bago a wajen taron, ya jaddada ƙaruwar barazanar da ‘yan ta’adda ke haddasawa ta hanyar dasa bama-bamai inda ya bayyana cewa sojoji na ci gaba da ƙoƙarin yaƙi da ‘yan bindiga.
Ya sake tabbatar da irin jajircewa da ƙoƙarin da Gwamna Bago da sojoji ke yi na tsaftace yankunan Shiroro daga bama-bamai da sauran ababen fashewa da 'yan ta'adda suka dasa.
Shugaban sansanin 013 na rundunar sojin sama Austine Idoko, ya ba da tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na tsaro domin kawar da ta’addanci da ‘yan bindiga daga jihar.
Ko a ranar 19 ga watan Disamban 2024, sai da jaridar Daily Trust ta ruwaito tashin wasu bama-bamai guda uku a Bassa da ke karamar hukumar Shiroro, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu biyar.
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Neja
A wani rahoto na baya-bayannan da Legit Hausa ta wallafa, kun karanta yadda jami'an rundunar sojin saman Najeriya suka yi ruwan bama-bamai a wasu sansanonin 'yan ta'adda da ke dajin Alawa a ƙaramar hukumar Shiroron jihar.
Sojojin dai sun kai waɗannan hare-haren ne da zummar halaka wasu hatsabiban 'yan ta'adda da suka addabi yankin da ayyukan ta'addanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng