APC Ta Yi Babban Rashi, Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Jagoran Jam'iyya Mai Mulki

APC Ta Yi Babban Rashi, Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Jagoran Jam'iyya Mai Mulki

  • Wasu miyagun ƴan bindiga da ake tsammanin ƴan kungiyar asiri ne sun kashe jigon APC a jihar Ondo, Fisayo Oladibo ranar Litinin, 6 ga watan Janairu
  • Marigayin tsohon shugaban matasan APC ne a ƙaramar hukumar Owo kuma ya taɓa tsayawa takarar ciyaman a mulkin marigayi Rotimi Akeredolu
  • Wannan babbar illa da aka yi wa jam'iyyar APC mai mulki ta zo ne a lokacin da ake jimami da alhinin rasuwar sakataren gwamnatin Ondo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Wasu miyagun ƴan bindiga da ake kyautata zaton ƴan kungiyar asiri ne sun hallaka wani babban jigon jam'iyyar APC a jihar Ondo, Fisayo Oladipo.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe Mista Oladipo, tsohon shugaban matasan APC a garin Owo, da ke ƙaramar hukumar Owo a jihar da ke Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Tsohon sakataren gwamnatin jiha a Najeriya ya rasu

Taswirar jihar Ondo.
Wasu miyagu sun kashe wani jigon APC a jihar Ondo, Fisayo Oladipo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yan bindiga sun kashe jigon APC

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa miyagun maharan sun yi ajalin Fisayo Oladipo ɗan kimanin shekaru 52 a safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayi jigon jam’iyyar APC ya taɓa neman takarar shugabancin karamar hukumarsa a zamanin gwamnatin marigayi tsohon Gwamna Oluwarotimi Akeredolu.

Wannan lamari na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan mutuwar sakataren gwamnatin Ondo, Temitayo Oluwatuyi Oluseye.

Jam'iyyar APC ta yi babban rashi a Ondo

Legit Hausa ta tattaro cewa marigayi Oluseye ya rasu ne sakamakon raunukan da ya ji a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi.

Sakataren gwamnatin ya gamu da hatsarin ne a tsakiyar watan Disamba, 2024 kuma Allah ya karɓi rayuwarsa ne ranar Asabar, 4 ga watan Janairu, 2025.

Kwanaki biyu bayan rasuwar SSG ne kuma miyagun suka hallaka jigon APC, lamarom da ya haifar da rikici da tashin hankali a garin Oyo.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'addan ISWAP, an tura miyagu da dama barzahu

Jami'an tsaro sun kai ɗauki garin Owo

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa yanzu haka hukumomin tsaro sun tura dakarunsu domin tabbatar da zaman lafiya da daƙile duk wata barazanar tada zaune tsaye.

Har yanzu dai ba a san maƙsudin kashe jagoran APC ba, amma an bayyana cewa tuni aka kai gawarsa dakin ajiye gawarwaki.

Bugu da ƙari, kwamandan hukumar tsaro ta sibil defens watau NSCDC, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Ya ce sun yi ƙoƙarin kwantar da hankulan mazauna garin Owo bayan jibge jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana.

“Ina mai tabbatar maku da cewa mun tura mutanenmu domin su taimaka wa sauran jami’an hukumomin tsaro da aka tura don kwantar da hankula jama'a," in ji shi.

Sai dai wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa an kashe wasu mutne da dama garin da rikicim ƴan kungiyoyin asiri ya ɓarke bayan kisan jigon APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Sakataren gwamnatin jiha a Najeriya ya rasu bayan ya gamu da hatsarin mota

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da limami

A wani rahoton, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da limamin coci, Cannon Olowolagba tare da matarsa da ƴaƴanta guda biyu.

Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kira ƴan uwan limamin cocin kuma sun nemi a tattara masu Naira miliyan 75 a matsayin kudin fansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262