Ministan Harkokin Wajen China Zai Ziyarci Najeriya da Wasu Kasashen Afrika

Ministan Harkokin Wajen China Zai Ziyarci Najeriya da Wasu Kasashen Afrika

  • Ministan harkokin wajen kasar China mai suna Wáng Yì zai fara rangadi na ziyara a Najeriya da wasu kasashen Afrika
  • Ziyarar na da nufin karfafa dangantakar China da kasashen Afrika a kan batutuwan ci gaban tattalin arziki da siyasa
  • Wannan rangadi yana zuwa ne a lokacin da China ke kokarin kara tabbatar da matsayinta na babbar kawar Afrika a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan harkokin wajen kasar China, Wáng Yì yana shirin gudanar da rangadi a wasu kasashen Afrika, ciki har da Najeriya, domin karfafa dangantakar diplomasiyya da tattalin arziki.

Ziyarar, wacce aka tsara a wannan watan, na zuwa ne a wani lokaci mai muhimmanci yayin da kasar China ke kara bayar da fifiko kan kyautata dangantaka da nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

Abin fashewa da ake zaton 'bom' ne ya tarwatse a makarantar islamiyya, ɗalibai sun mutu

China Yi
Ministan warkokin wajen China zai ziyarci Najeriya. Hoto: Pool
Asali: Getty Images

Punch ta rahoto cewa rangadin ya samu karbuwa daga gwamnoni da masu ruwa da tsaki a Najeriya, da suke ganin hakan wata dama ce ta kara samun ci gaba a fannonin tattali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ziyarar Yi a Afrika ta kunsa

Legit ta rahoto cewa ziyarar Wáng Yì za ta mayar da hankali kan tattaunawa da shugabanni a Najeriya kan alakar tattalin arziki da batutuwan da suka shafi cinikayya, zuba jari, da dangantakar siyasa.

Kazalika, ana sa ran Ministan zai tattauna batutuwan tsaro, musamman a fannin yaki da ta’addanci da samar da kwanciyar hankali a yankin.

Bugu da kari, Yi zai gabatar da wasu sababbin tsare-tsare da gwamnatin kasar China ta tanadar domin kara bunkasa ayyukan hadin gwiwa tsakanin Afrika da kasar Sin.

“Ziyarar wannan karo ba kawai ta mayar da hankali kan tattalin arziki da cinikayya ba, har ma tana dauke da batutuwan al’adu da zaman lafiya.”

Kara karanta wannan

Bayar da rance ga talaka da wasu muhimman abubuwa 9 da Tinubu zai aiwatar a 2025

- Mao Ning, kakakin ma'aikatar harkokin wajen China

Muhimmancin ziyarar ga Najeriya da Afrika

Ziyarar Yi na da muhimmanci ga Najeriya, kasancewar kasar ita ce babbar kawar China a nahiyar Afrika.

Najeriya tana da huldar cinikayya mai karfi da kasar China, musamman a bangaren zuba jari a fannin kayayyakin more rayuwa kamar hanyoyi, gidaje, da tashoshin jiragen ruwa.

Bugu da kari, kasar China ta kasance daya daga cikin manyan kasashe masu sayen albarkatun kasa daga Najeriya.

Masana na ganin cewa ziyarar za ta kara tabbatar da cewa Najeriya tana da mahimmanci a jerin kasashen da China ke fifitawa wajen huldar kasuwanci da siyasa.

Matsayin kasar China a nahiyar Afrika

A shekaru da dama da suka gabata, China ta kasance babbar kawar Afrika a duniya, musamman wajen samar da rancen kudi da zuba jari a fannin bunkasa tattalin arziki.

Daga cikin kasashen da za su amfana daga wannan ziyara, Najeriya tana kan gaba, kasancewar ta cikin kasashe masu karfi a nahiyar wajen tattalin arziki da yawan jama’a.

Kara karanta wannan

Ta ku ta kare: Sojoji sun shirya tsaf za su ga karshen 'yan ta'addan Najeriya a 2025

Ministan harkokin wajen kasar China zai kuma tattauna kan batutuwan kasa da kasa, da yadda za a ci gaba da kyautata dangantakar Afrika da China a cikin tsarin siyasar duniya.

A wannan ziyarar, ministan zai ziyarci:

  • Najeriya
  • Namibia
  • Congo
  • Chadi

Najeriya ta sake yarjejeniyar kudi da China

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya da China sun kara tabbatar da yarjejeniyar Naira da Yuan da suka kulla.

Rahotanni sun nuna cewa tun a shekarar 2018 kasashen suka kulla yarjejeniyar kuma a yanzu haka za a kara nausawa gaba har tsawon shekaru uku cikinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel