Kwamitin Kudirin Haraji Ya Gana da Malamai 120 domin Neman Goyon Baya
- Shugaban Kwamitin tsare-tsaren kudi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele, ya bayyana dalilin da yasa gwamna na jihar Lagos kadai ya gana da kwamitinsa
- Rahotanni sun nuna cewa Taiwo Oyedele ya karyata zargin cewa ba a tattauna da gwamnonin jihohi game da kudirin gyaran haraji ba
- Hakan na zuwa ne yayin da wasu gwamnoni ke nuna adawa da kudirin harajin suna mai cewa za su yi illa ga lamuran tattalin jihohinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsaren kudi da haraji, Taiwo Oyedele, ya jaddada bukatar gudanar da tarukan shawara a duk fadin kasa game da kudirin haraji.
Oyedele ya bayyana cewa kwamitinsa ya yi kokarin ganawa da gwamnonin jihohi amma sau hudu ana shirya zama ana soke su.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Oyedele ya ce gwamnan jihar Lagos ne kadai ya amsa gayyatar kwamitin daga cikin gwamnonin da aka bukaci ganawa da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me yasa gwamna 1 ya gana da kwamitin haraji?
A cewar Oyedele, kwamitin ya rubuta wasiku domin ganawa da gwamna daya daga kowanne yanki na kasar nan.
Amma duk da kokarin, Oyedele ya ce har zuwa yanzu, gwamna na jihar Lagos ne suka yi nasarar ganawa da shi.
Kwamitin haraji ya gana da malamai 120
Ya ce sun gana da shugabanni daga bangarori daban-daban, ciki har da malaman addini daga yankin Arewa da kuma kungiyar NLD, domin bayyana manufar kudirin harajin.
“Mun gana da malamai sama da 120 daga yankin Arewa. Mun yi bayani dalla-dalla kan kudirin haraji,
kuma daga bisani da dama daga cikinsu sun yi mana addu’a saboda an sun tattabar da cewa an cusa bayanai marasa inganci wajen bayani a kan kudirin.”
- Taiwo Oyedele
Adawar wasu gwamnonin Arewa
Wasu gwamnonin Arewa sun nuna adawa da wasu bangarorin tsare-tsaren haraji, suna masu cewa za su shafi kudin shigar jihohinsu.
Sai dai Oyedele ya bayyana cewa gyaran harajin zai tabbatar da tsarin haraji mai inganci da adalci wanda zai inganta ci gaban kasa baki daya.
Martani ga Buba Galadima kan haraji
A baya, dattijo kuma dan siyasa daga yankin Arewa, Buba Galadima, ya yi ikirarin cewa wasu mambobin kwamitin sun nesanta kansu daga rahoton kudirin.
A cewar Buba Galadima, wasu mambobin kwamitin suna cewa ba a tuntube su ba kafin yanke shawarar kan kudirin da aka tsara.
Sai dai Oyedele ya musanta wannan zargi, yana mai cewa kwamitin zai ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa an samu nasarar aiwatar da gyaran harajin.
Kiran neman hadin kai daga kwamitin
Oyedele ya yi kira ga gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki da su bayar da gudummawarsu domin tabbatar da samun tsarin haraji mai adalci da zai amfani daukacin kasa.
Arise News ta wallafa cewa kwamitin ya ce yana da cikakken shiri na sauraron korafe-korafe da gyara duk wata matsala da za ta iya tasowa daga kudirin gyaran harajin.
Tinubu ya turo wakilai Arewa kan haraji
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cigaba da kokarin ganin kudirin haraji ya samu karbuwa a Arewa.
A wani sabon mataki da ya dauka, shugaba Tinubu ya turo wakilai Arewacin Najeriya da za su zauna da manyan domin neman goyon bayan kudirin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng