Kudirin Haraji: Kwamitin Gwamnatin Tinubu Ya Karyata Zargin Dattawan Arewa
- Kwamitin Shugaban kasa a kan gyara tsarin kudi da gyaran haraji ya caccaki kalaman dattawan Arewa a kan kudirorin haraji
- Shugaban kwamitin, Taiyo Oyedele ya bayyana cewa sai da suka tattauna da malaman addini da sauran kusoshi a Arewa kan batun
- Wannan martani ne ga kalaman dattawan Arewa dake zargin kwamitin ya gana da gwamnan Legas, Babajide Sanwo Olu ne kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Tsarin Kuɗi da Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele, ya musanta zargin cewa kwamitin bai tuntubi gwamnonin Najeriya ba kan kudirin haraji ba.
Oyedele ya kuma bayyana cewa kwamitin ya gana da akalla malaman addini Musulmi 120, mafi yawan su daga Arewacin Najeriya, sannan sun yi yunkurin ganawa da sauran masu ruwa ta tsaki.
Taiwo Oyedele ya shaida wa Arise News cewa gwamnatocin jihohi sun soke tarukan da aka shirya sau huɗu dmin tattauna batutuwan da su ka shafi kudirin haraji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A gefe guda kuma ya ce sun tattauna da ƙungiyar ‘League of Democrats’ domin fayyace tasirin gyaran tsarin harajin da ake gudanarwa.
Dattawan Arewa sun soki kudirin haraji
Dattijon dan siyasa a Arewacin kasar nan, Buba Galadima, ya ce dokokin harajin Tinubu za su amfanar da jihohin Ogun da Lagos ne kawai.
Ya kuma yi zargin cewa kwamitin da Oyedele ke jagoranta bai gana da kowanne gwamna ba sai na jihar Lagos kadai zuwa lokacin da aka kammala kudirin harajin.
Oyedele ya soki dattawan Arewa
Oyedele, wanda ya musanta zargin Galadima, ya bayyana cewa kwamitin da aka kafa a ranar 8 ga Agusta, 2023, ya ƙunshi mambobi da yawa daga dukkan yankunan siyasa na ƙasar.
Ya bayyana cewa sai da suka rika kokarin ganawa da gwamnoni, amma su ka ki amincewa da tsayar da lokacin da za a tattauna sauran batutuwan da suka shafi kudirin haraji.
“Muna da fiye da hukumomin gwamnati 20 da ke da wakilci. Muna da masu zaman kansu, kama daga masana'antu zuwa mata masu kasuwanci. Muna da ɗalibai 45 daga jami’o’i 22 a faɗin Najeriya.
“Baya ga haka, mun yi tattaunawa mai zurfi da gwamnonin jihohi. Na ziyarci kungiyar gwamnonin Najeriya. Mun rubuta wasiƙa kuma muna son mu gana da gwamna ɗaya daga kowanne yanki shida na ƙasa. Zuwa yanzu, gwamnan jihar Lagos kawai muka samu damar gani.”
Tinubu ya aika tawaga zuwa Arewa
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tashi tawaga zuwa Arewacin Najeriya domin a taushi manyanta wajen amincewa da dokar harajin da ya aika ga majalisar dokokin kasar nan.
Shugaban Gwamnonin Arewa, Gwamna Muhammad Yahaya ya sake jaddada matsayinsu na rashin amincewa da kudirin gyaran haraji, duk da ƙoƙarin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, na samun goyon bayansu.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Tinubu yana tuntubar wasu daga manyan 'yan siyasar Arewa domin samun goyon bayansu ganin yadda shugabannin Arewa suka bijere masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng