'Yan Bindiga Sun Taso Mutanen Zamfara a Gaba, Sun Saka Haraji Mai Tsoka
- Ƴan bindiga sun saka rayuwar mutanen ƙauyukan Tsafe ta Yamma cikin barazana bayan sun lafta musu haraji mai tsoka
- Tsagerun waɗanda suka aiki a ƙarƙashin jagorancin shugabansu Danisuhu, sun sanya harajin N172m ga ƙauyuka 25 na ƙaramar hukumar Tsafe
- Sanya harajin da ƴan bindigan suka yi ya tilastawa jama'a yin ƙaura daga gidajensu saboda gudun abin da zai biyo baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun lafta haraji mai tsoka kan mutanen wasu ƙauyuka a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan da ke aiki a ƙarƙashin jagorancin wani tantirin shugabansu da aka fi sani da Danisuhu sun sanya harajin N172,700,000 kan ƙauyuka 25 da ke yankin Tsafe ta Yamma a jihar Zamfara.
Ƴan bindiga sun sanya haraji a Zamfara
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanya harajin da ƴan bindigan suka yi ya ƙara jefa al’ummar ƙauyukan cikin mawuyacin hali na rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi.
Majiyoyi sun bayyana cewa sanya harajin tare da buƙatar ba da kayayyakin noma kamar kamar buhunan wake, na tattare da barazanar tashin hankali, lamarin da ya sa mazauna yankin da dama suka bar gidajensu.
Yanzu haka ƙauyuka da dama a yankin sun zama babu kowa, bayan mutane sun yi ƙaura daga gidajensu.
Harajin da kowane ƙauye zai biya
Ƙauyukan da aka sanyawa harajin sun haɗa da Gijinzama: N8.5M, Dakolo: N5m da buhun wake 20, Gunja: N7m, Kauyen Kane: N5m, Kurar Mota: N6m, Sabon Garin Bakin Gulbi: N5m, Kibari: N3m, da Karda: N5m.
Sauran su ne Daga Ciki: N3m, Biya: N5m, Barebari: N6m, Kauyen Magaji: N7m, Kwaren Maisaje: N10m, Magazawa: N10m, Maciya: N5m, Unguwar Danhalima: N5m.
Ragowar sun haɗa da Unguwar Rogo: N5m, Katanga: N5m, Magazu: N5m, Sungawa: N15m, Rakyabu: N15m, Yalwa: N2.7m, Tsageru: N5m, Gidan Anne: N7m, Kunchin Kalgo: N20m.
Mutane sun bar gidajensu a Zamfara
Rahotanni sun nuna cewa ɗaruruwan mazauna waɗannan ƙauyuka sun bar gidajensu, filayen noma, saboda fargabar tashin hankalin da zai biyo baya kan gaza cika sharuɗɗan.
"Al'amarin yana da muni. Rashin biyan waɗannan kuɗaɗen haraji ya kan haifar da munanan hare-hare daga ƴan bindigan, wanda hakan yake sanya mutane su gudu saboda ba su da wani zaɓi."
"A yayin da aka samu ingantuwar tsaro a kan titin Funtua-Tsafe da kuma garin Tsafe, har yanzu waɗannan nasarorin ba su kai ga ƙauyukan Tsafe ta Yamma ba."
- Wata majiya
Mutanen ƙauyukan dai sun buƙaci mahukuntan Najeriya da su kai musu ɗaukin gaggawa ta hanyar tura ƙarin jami'an tsaro a yankin Tsafe ta Yamma.
Ƴan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsagerun ƴan bindiga sun hallaka shugaban riƙon ƙwarya na ƙungiyar Miyetti Allah a jihar Ƙatsina.
Ƴan bindigan sun hallaka Alhaji Amadu Surajo a wani mummunan hari da suka kai a gidansa da ke ƙauyen Mai Rana a ƙaramar hukumar Kusada.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng