Zamba: Hukumar Yaki da Rashawa, Jami'in gwamnatin Ganduje na Musayar Yawu

Zamba: Hukumar Yaki da Rashawa, Jami'in gwamnatin Ganduje na Musayar Yawu

  • Tsohon Manajan Daraktan KASCO, Bala Inuwa ya caccaki hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano bisa zargin watsi da umarnin kotu
  • Lauyansa, Ibrahim Tahir Esq ya ce sun samu umarnin kotu da ya haramtawa hukumar PCACC ta kano taba kadarorin Bala Inuwa
  • Amma tuni hukumar yaki da rashawa ta yi martani, inda ta zargi tsohon Manajan Daraktan ya nemi umarnin kotu ta haramtacciyar hanya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Zazzafan musayar yawu ya kunno kai tsakanin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) da Bala Inuwa, tsohon Manajan Daraktan KASCO,.

Hukumar PCACC ta na zargin Bala Inuwa da mallakar wasu kadarori ta hanyar almundahana da kudin fa ya samu ta haramtacciyar hanya da ya kai kimanin Naira biliyan hudu.

Kara karanta wannan

Tinubu na ganin sabuwar matsala daga Arewa, dattawa sun ƙi yarda da gyaran haraji

Muhuyi
PCACC, Bashir Inuwa na zargin juna da karya doka Hoto: Muhuyi Magaji Rimin Gado
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Hukumar ta PCACC ta bayyana cewa kadarorin da PCACC ta kama sun kunshi gidaje da wasu muhimman kadarori wanda ta ce an samo su daga kudaden haram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan zargi ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin bangarorin biyu, inda Bala Inuwa ke musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa tare da zargin hukumar PCACC da karya doka.

An zargi hukumar PCACC da take doka

Jaridar Punch ta wallafa cewa lauyan tsohon Manajan Daraktan hukumar KASCO, Ibrahim Tahir Esq ya zargi shugaban hukumar PCACC na Kano da fatali da umarnin kotu.

Ya bayyana cewa an samu umarnin kotun da ya haramtawa hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa na Kano hana taba kadarorin tsohon shugaban KASCO da ake takaddama a kansu.

Ibrahim Tahir Esq ya ce amma hukumar yaki da rashwa ta Kano ta yi watsi da umarnin kotu, wanda ya ke daidai da karya dokar kasa, da rashin mutunta dokokin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da jarumar Kannywood, an fadi dalili

Martanin hukumar PCACC

Da yake karin bayani, shugaban PCACC, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya ce hukumar ta yi aiki ne bisa ga huruminta na doka wajen gano duk wani abu da ke da alaka da zamba ko kudaden haram.

Sakataren hukumar da ke ba da shawara kan doka, Zahraddeen Hamisu Kofar Mata, zargi tsohon shugaban na KASCO da ya shigar da karar da ta saba doka gaban Mai Shari’a Aisha Yau.

Ya bayyana cewa hukumar ta maka tsohon MD a gaban Mai Shari’a Hafsat Yahaya ta babbar kotu mai lamba 11 bisa tuhumar hada baki da kuma almundahana, inda ake ci gaba da shari'a.

PCACC ta fara binciken Ciyamomi

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta tsare shugabannin kananan hukumomi uku kan zargin aikata badaƙalar kwangilar ruwa ta kimanin N660m.

Daga cikin wanda aka tsare akwai Musa Garba Kwankwaso, wanda aka ba da belinsa a ranar Alhamis da misalin karfe 9.00 na dare bayan ya bayyana a gaban hukumar, inda ake zargin an amince ya koma ofishinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.