Gwamna Radda Ya Yabawa Sojoji bayan Samun Muhimmiyar Nasara kan 'Yan Bindiga
- Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Dikko Umaru Radda, ta nuna farin cikinta kan nasarorin da dakarun sojoji suka samu a kan ƴan bindiga
- Dakarun sojojin dai tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga 80 tare da lalata sansanoninsu a Jibia
- Gwamna Dikko Radda ya yabawa jami'an tsaron bisa wannan nasarar da suka samu kan ƴan bindigan da suka addabi jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda, ta yabawa dakarun sojoji kan ragargazar ƴan bindiga.
Gwamnatin ta yabawa sojojin sama na rundunar Operation Fansan Yamma, dakarun sojojin runduna ta 17, ƴan sanda, DSS, jami'an KSWC da ƴan sa-kai kan nasarar da suka samu a kan ƴan bindiga.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasir Mu'azu ya fitar, wacce hadimin gwamna, Isah Miqdad ya sanya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Dikko Radda ya yabawa sojoji
Gwamna Dikko Radda ya yabawa jami'an tsaron ne kan hare-haren da suka kai a sansanonin ƴan bindiga da ke yankunan Kadoji, Matso- Matso, Bagga, Dogon Marke da Takatsaba na ƙaramar hukumar Jibia.
Hare-haren, wanda aka kai ranar Asabar, 4 ga Janairu 2025, sun biyo bayan bayanan sirri da suka tabbatar da kafa sansanonin ƴan bindiga a yankin Jibia.
Kafa waɗannan sansanoni ya ƙara ta’azzara ayyukan ƴan bindiga a ƙananan hukumomin Jibia, Batsari, da Batagarawa, wanda hakan ya yi matuƙar tayar da hankali ga al’ummomin yankunan.
Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga a Katsina
Hadin gwiwar sojojin sama da na kasa a hare-haren ya kai ga hallaka ƴan bindiga 80, tare da raunata wasu da dama daga cikinsu.
Bugu da ƙari, an lalata maɓoyarsu da muhimman kayan aikinsu, wanda hakan ya zama babban koma-baya ga ƙarfin ƴan bindigan na kai hare-hare.
"Gwamnatin Jihar Katsina tana mika godiya mai zurfi ga jajircewar tawagar tsaro ta hadaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kuma yankin Arewa maso Yamma baki daya."
- Nasiru Mu'azu
Gwamnatin Katsina za ta ba jami'an tsaro goyon baya
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da goyon bayan jami’an tsaro ta hanyoyi daban-daban don tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a jihar.
Wannan nasara na daga cikin alƙawarin Gwamna Dikko Radda na tabbatar da tsaro da ci gaban jihar Katsina tun bayan hawansa mulki.
A karshe, gwamnati ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da ba da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro domin ganin an kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a jihar da kewaye.
Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina, sun samu nasarar daƙile wasu hare-hare da ƴan bindiga suka kai kan matafiya.
Jami'an ƴan sandan sun kuɓutar da mutane 18 bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da su cikin dare a kan hanyar Funtua zuwa Gusau.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng