Abba Ya Yi Sababbin Nade Nade, Mutum 5 Sun Samu Manyan Mukamai a Gwamnatin Kano

Abba Ya Yi Sababbin Nade Nade, Mutum 5 Sun Samu Manyan Mukamai a Gwamnatin Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada sababbin masu ba da shawara na musamman, ciki har da Hon. Ahmad Speaker da Injiniya Ahmad
  • An shirya gudanar da bikin rantsar da wadanda aka nada a ranar Litinin, 6 ga Janairu, a gidan gwamnatin Kano da karfe 11:00 na safe
  • Haka zalika, gwamnatin Kano ta yi bayani game da lokacin da mai girma Abba zai rantsar da sabbin kwamishinoni bakwai da ya nada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da jerin wasu nade-nade don karfafa cigaban gudanarwar gwamnatinsa.

Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamna Abba ne ya sanar da hakan a ranar Lahadi, 5 ga watan Janairun 2025.

Gwamnatin Kano ta yi magana yayin da Abba ya nada sababbin masu ba shi shawara
Gwamnan Kano, Abba ya yi sababbin nade nade, an fitar da jerin sunaye. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Gwamnan Kano ya yi sababbin nade nade

A sanarwar da ya fitar a shafinsa na Facebook, Sanusi Bature ya ce nade-naden za su fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Sarki a Najeriya ya gamu mummunan hatsari, Allah ya yi masa rasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda aka nada, akwai Hon. Ahmad Muhammad Speaker a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan yada labarai.

Hon. Ahmad ya kasance tsohon shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa har sau uku, kuma tsohon sakataren tsare-tsare na APC a Kano.

An nada ma su ba gwamna shawara

Gwamna ya nada Injiniya Ahmad a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan ayyuka, da nufin mai da hankali kan cigaban ababen more rayuwa.

Bugu da kari, Malam Sani Abdullahi Tofa ya samu mukamin mai ba Abba shawara na musamman kan ayyuka na musamman.

Malam Sani Tofa, tsohon Khadi ne na Kotun Shari’a a Kano da Abuja, kuma tsohon babban sakataren dindindin na Kano.

Malam Tofa ya kasance tsohon darakta janar na hukumar shari’a ta Kano, wanda ya bar aiki da babbar kwarewa.

Abba ya ba tsofaffin kwamishinoni mukami

Hakazalika, an nada Hon. Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

An kuma nada Hajiya Ladidi Ibrahim Garko a matsayin Shugabar Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar Kano.

Hon. Ibrahim Jibrin da Hajiya Ladidi Ibrahim sun kasance tsoffin kwamishinoni biyu - na ma’aikatar kudi da na yawon bude ido.

An sanya ranar rantsar da kwamishinoni 7

Gwamnan ya ce za a yi bikin rantsar da su a ranar Litinin, 6 ga Janairu, 2025 da karfe 11:00 na safe a gidan gwamnati.

Bikin zai kuma hada da rantsar da kwamishinoni bakwai da majalisar dokoki ta Kano ta tantance kwanan nan.

Wadannan nade-nade sun nuna himmar Gwamna Yusuf wajen dora kwararrun mutane a kan mukamai domin cigaban jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.