'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga, Sun Kubutar da Mutane a Katsina
- Jami'an rundunar ƴan sandan jihar sun samu nasarar daƙile hare-haren ƴan bindiga a wurare har guda biyu
- Ƴan sandan sun kuɓutar da mutane 18 da ƴan bindiga suka sace a kan hanyar Funtua zuwa Gusau a cikin dare
- Jami'an tsaron sun kuma ɗaƙile yunƙurin ƴan bindiga na sace shanu masu yawa bayan sun yi musayar wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ceto aƙalla mutane 18 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.
Jami'an ƴan sandan sun ceto mutanen ne bayan daƙile harin ƴan bindiga a hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara.
Ƴan sanda sun fafata da ƴan bindiga
Tashar Channels tv ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ƴan sandan ta kuma yi nasarar ƙwato shanu masu yawa bayan daƙile yunƙurin satarsu a ƙauyen Gidan Gada da ke ƙaramar hukumar Kafur.
Kakakin ƴan sandan ya ce an yi yunƙurin yin garkuwa da mutanen ne a ranar 3 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 9:30 na dare, bayan ƴan bindiga sun yi wa motoci huɗu kwanton ɓauna a hanyar Funtua-Gusau.
Ƴan sanda sun daƙile hare-haren ƴan bindiga
"Bayan samun rahoton, DPO na ƴan sandan Faskari, ya tattara jami’ai zuwa wurin da lamarin ya faru, inda aka yi musayar wuta."
"Jami'an rundunar sun samu nasarar daƙile harin da ƴan bindigan suka kai tare da ceto mutane 18 da lamarin ya rutsa da su."
"Hakazalika a wannan ranar da misalin karfe 11:00 na dare wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Gidan Gada da ke ƙaramar hukumar Kafur a jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da wasu shanu."
"Bayan samun rahoton, DPO na Kafur da Malumfashi sun tattara jami'ai tare da bin sahun ƴan bindigan zuwa ƙauyen Fanisau, inda suka yi artabu da ɓarayin, tare da nasarar ƙwato dukkanin dabbobin da aka sace."
"Sai dai abin takaici DPO Kafur ya samu raunin harbin bindiga a yayin arangamar kuma nan take aka garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa, kuma a halin yanzu yana samun sauƙi."
- ASP Abubakar Sadiq Aliyu
Ƴan sanda sun yi bajinta
Zaharaddeen Aminu ya shaidawa Legit Hausa cewa jami'an ƴan sandan sun yi bajinta sosai wajen daƙile harin tsagerun ƴan bindigan.
"Wannan abin a yaba ne sosai. Gaskiya jami'an ƴan sandan sun yi ƙoƙari. Muna yi musu addu'ar Allah ya ci gaba da ba su nasara kan miyagu."
- Zaharaddeen Aminu
Ƴan sanda sun cafke jami'in tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Borno, sun samu nasarar cafke wani ɗan banga mai taimakon ƴan ta'addan Boko Haram.
Jami'an ƴan sandan sun cafke ɗan bangan ne bisa zarginsa da samar da kayayyakin amfanin yau da kullum ga ƴan ta'addan masu tayar da ƙayar baya.
Asali: Legit.ng