Arewa Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban Jami’o'in Sokoto da Abuja Ya Rasu

Arewa Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban Jami’o'in Sokoto da Abuja Ya Rasu

  • An shiga wani irin yanayi bayan rasuwar tsohon shugaban Jami'ar Abuja, Farfesa Nuhu Yaqub bayan fama da jinya
  • Daraktan hukumar NILDS, Farfesa Abubakar Sulaiman, ya jajanta rasuwar marigayin Nuhu Yaqub wanda ya rasu ranar Asabar
  • Farfesa Sulaiman ya bayyana marigayin a matsayin ƙwararren malami kuma tsohon Shugaban Jami’o’in Sokoto da Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Daraktan Hukumar (NILDS), Farfesa Abubakar O. Sulaiman ya kadu da rasuwar Farfesa Nuhu Yaqub.

Farfesa Sulaiman ya mika ta'aziyya bayan rasuwar tsohon shugaban Jami'ar Abuja da ke Arewacin Najeriya.

Tsohon shugaban Jami'ar Abuja ya kwanta dama
Tsohon shugaban Jami'ar Abuja, Farfesa Nuhu Yaqub ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: Aros Oyarazi Sadiq.
Asali: Facebook

Tsohon shugaban Jami'ar Abuja ya rasu

Leadership ta ce Farfesa Yaqub, Shugaban Hukumar Shawarar Ilimi a NILDS, ya rasu a ranar Asabar 4 ga watan Janairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Sulaiman ya bayyana mutuwar Farfesa Yaqub a matsayin abin ban mamaki da kuma tashin hankali.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

Ya yabi marigayin inda ya bayyana shi a matsayin fitaccen malami kuma tsohon Shugaban Jami’ar Jahar Sokoto da Jami’ar Abuja, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ilimi da bincike a Najeriya.

Gudunmawar da Farfesa Yaqub ya bayar

A cewarsa, Farfesa Yaqub ya bayar da gagarumar gudunmawa a fannin ilimi, yana da tasiri kan ɗalibai da masu tsara manufofi.

Farfesa Sulaiman ya koka da cewa wannan malami mai ƙwarewa da ɗan siyasa ya bar duniya a lokacin da ake matuƙar buƙatar iliminsa.

Daraktan NILDS ya ƙara bayyana cewa mutuwar marigayin babban rashi ne gare shi a matsayin mutum, tare da bayyana jihar Kogi a matsayin wadda ta yi babban rashi a harkar ilimi.

Ya miƙa ta’aziyya ga matar marigayin, ’ya’yansa, danginsa, gwamnatin Jihar Kogi, da al’ummomin jami’o’i a faɗin ƙasar, cewar Tribune.

Sakataren gwamnatin jihar Ondo ya rasu

Kun ji cewa Sakataren Gwamnatin jihar Ondo, Temitayo Oluwatuyi Oluseye ya yi bankwana da duniya bayan fama da raunin haɗarin mota.

An nada Oluseye a matsayin SSG a ranar 24 ga Janairu, 2024, kuma ya yi hidima da kwazo da jajircewa ga jiharsa har zuwa mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.